KORONA: Mutum 252 sun kamu ranar Talata, Yanzu mutum 52,800 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 252 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –26, Filato-50, Enugu-35, Rivers-27
FCT-18, Kaduna-18, Ekiti-10, Kano-10, Taraba-9, Anambra-8, Edo-8, Oyo-8, Delta-7, Ogun-6, Abia-5, Bayelsa-5, Ebonyi-1 da Osun-1.

Yanzu mutum 52,800 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 39,964 sun warke, 1007 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,829 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,018 FCT –5,046, Oyo – 3,058, Edo –2,553, Delta –1,715, Rivers 2,090, Kano –1,721, Ogun – 1,631, Kaduna –2,059, Katsina –771, Ondo –1,515, Borno –740, Gombe – 714, Bauchi – 644, Ebonyi – 965, Filato -2,18 5, Enugu – 1,087, Abia – 755, Imo – 523, Jigawa – 322, Kwara – 936, Bayelsa – 374, Nasarawa – 421 , Osun – 769, Sokoto – 156, Niger – 239, Akwa Ibom – 271, Benue – 451, Adamawa – 217, Anambra – 202, Kebbi – 92, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 235, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.

Yadda cin kwai ke samar wa mutum kariya daga kamuwa da cututtuka

Kungiyar masu kiwon kaji ta kasa ta yi kira ga mutane da su rika cin kwai a kullum ranar domin inganta karfin garkuwan jikin su.

Kungiyar ta ce samun karfin garkuwan jiki zai taimaka wajen kare mutum daga kamuwa da cututtuka musamman cutar Koronabairos da ya zama annoba a duniya.

Shugaban Kungiyar Ezekiel Ibrahim ya Sanar da haka Yana Mai cewa cin kwai akalla kwaya daya a duk rana na Samar wa mutum kariya daga kamuwa da cututtuka musamman Coronavirus.

Ibrahim ya ce kwai na dauke da sinadarori kamar su protein, calories, vitamins, minerals, carotenoids, saturated fat da iron wanda ke taimakawa wajen samar wa mutum kariya daga kamuwa da cututtuka.

Sannan kwai na dauke da sinadarin lutein da zeaxanthin wanda ke taimaka wa wajen rage matsalolin da ake samu idan an tsufa.

Ibrahim ya ce kwai abinci ne da babba da yaro za su rika ci a koda yaushe ba tare da an samu matsala ba.

Ya yi kira ga gwamnati da ta hada da kwai cikin kayan abincin da take tallafa wa mutane domin rage musu radadin zaman gida dole.

“Yana da mahimmanci idan gwamnati ta samar wa ma’aikatan kiwon lafiya dake aikin yaki da cutar kwai su na ci, ma’aikatan tashan jiragen sama da ruwa da ma’aikatar dake kula da gidajen Kasoa domin inganta karfin garkuwan jikinsu.

Share.

game da Author