Fitaccen dan wasan duniya wanda ya lashe kambun wanda yafi kowa iya murza tamola a duniya kuma dan kasar Argentina, wato Leo Messi ya rubuta wa kungiyarsa ta Barcelona cewa zai bar kulob din.
Kungiyar ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na AP cewa Messi ya aika mata da shimfidaddiyar wasika da ya bayyane cewa ya hakura da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
Tun bayan ragargazar kwallaye da yai a ragar ta a wasan ta da Bayern Munich Barcelona komai ya dague wa kungiyar. Fitaccen dan wasan ta Gerard Pique ya shaida cewa wannan kashi da kungiyar ta sha abar kunya ce kuma ya goyi bayan duk abinda kungiyar za ta yi domin sauya fasalin kungiyar tayi.
Hakan yasa da yawa ‘yan wasn kungiyar na sa aran za su waske. Sai dai ba ayi tunanin cewa Messi zai fice daga kungiyar ba.
Wadanda kuma ya zo ya samu su a Kulob dinne, Allah ya raka taki gona.
Discussion about this post