Babban Editan Jaridar Daily Trust, Naziru Abubakar, ya bayyana tare da yin gargadi ga tsohon ministan Sufuri, Fani Kayode cewa idan wani abu ya samu wakilin jaridar na Cross Rivers, Charles shine jaridar za ta tuhuma.
Fani Kayode yayi wa wakilin Daily Trust Charles, luguden kalaman batanci, inda ta inda yake hawa ba ta nan yake sauka ba saboda tambayarsa da yayi, wa ya dauki nauyin wannan balaguro da yake tayi daga wannan jiha zuwa wancan da sunan wai yana duba ayyukan da gwamnoni suka yi.
Abubakar ya kara da cewa Daily Trust na tare da wakilin ta 100 bisa 100 kuma basu ga inda ya karya dokar aiki ba ko ya ci mutuncin Fani Kayode akan tambayar da yayi masa.
” Bamu ga abin fada a ciki ba, daga wanna. tambaya ‘wa ya dauki nauyin zirga-zirgar da yake ta yi shi kenan kuma sai ya zama tashin hankali.
Bayan haka Abubakar ya yaba wa wakilin jaridar bisa kamala da ya nuna a lokacin da Fani Kayode yake ragargaza masa zage-zage a bainar ‘yan uwan sa ‘yan jarida.
An dai nuno wani bidiyo inda Fani-Kayode ke tashi a fusace ya fice daga dakin taron manema labarai, bayan ya ragargaza wa Eyo Charles, wakilin Daily Trust masifa a Kalaba.
Kayode ya ce wakilin Daily Trust ya yi masa tambayar rashin kunya, rashin ganin girman sa da kuma tambayar tozarta shi a idon duniya.
Lamarin ya faru a ranar Alhamis a wani otal a Kalaba, inda tsohon Ministan ya tara ‘yan jarida domin yi masu karin bayanin rangadin da ya ke yi a jihohin Kudu maso Kudu.
Tambayar Wakilin Daily Trust Da Ta Harzuka Femi Fani-Kayode:
Tambaya: Wakilin Daily Trust ya nemi sanin ko akwai wanda ke daukar rangadin da Femi ke yi a jihohin da ya karaaina.
Femi: “Wace irin tambayar banza da wofi ce ka ke yi min? Wa ke daukar nauyin wa? Ni ake daukar nauyi na? Shin ka kuwa san da wanda ka ke magana kuwa?” Inji Femi Fani-Kayode a fusace.
Daga nan ya waiwaya ya kalli kakakin yada labarai na Gwamna Ayade, wanda ke zaune kusa da shi, ya ce ba zai sake amsa wata tambaya daga bakin Charles ba.
Daga nan kakakin yada labarai Its ya rika ba shi hakuri, ya na cewa, “hucewa yallabai”, amma dai Femi Fani-Kayode bai hakura ba.
“Na lura da fuskar ka tun ma kafin a shigo zauren taron nan, kai mutumin banza ne. Kada is sake yi min irin wannan zancen wofin.”
Wakilin Daily Trust dai na tsaye, bai sake cewa komai ba. Sai da Femi Fani-Kayode ya gama surfa masa zagi, sannan ya ce buda baki ya ce masa, “hucewa yallabai.”
Kamar ya kara hura wa Femi Fani-Kayode wuta, sai tsohon ministan ya sake cewa, “kada ka dauka daidai na ke da shashasha irin ka. Tun cikin 1990 na shiga siyasa. Babu irin gwagwarmaya da daurin da ba a yi min ba. Ba kamar irin ‘yan siyasar da ku ke bi ku na yi musu maula ba.
“Ni ba matsiyaci ba ne. Ba na rokon wani ya ba ni kudi. Ban taba roko ba, kuma ba zan taba rokon kowa ba.”
Daga nan babu wanda ya kara yi masa wata tambaya, sai ya tashi ya fice a fusace.
“Ya shamamce ni” -Wakilin Daily Trust
Charles ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Fani Kayode ya shammace shi, ya rasa ma yadda zai yi, shi ya sa kawai ya ce masa ya yi hakuri.
Sai dai kuma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ‘yan jarida sun rika cewa bai kamata ya yi masa irin tambayar da ya yi masa din ba.
Ya ce bai yi tsammanin Femi Fani-Kayode zai hau shi da hargagi da zage-zage irin na ‘yan jagaliya ba.
“Ni fa tambayar sa na yi cewa: Yallabai ka ce ka yi rangadin jihohi shida ko bakwai. Yanzu ga shi ka kammala rangadin ka a Cross River ka ga ayyukan da wadannan gwamnoni suka yi. Shin wa ke daukar nauyin wannan rangadi da ka yi?”
Ya ce bayan taro ya watse ba shiri, wani jami’in tsaron Femi Fani-Kayode ya same shi ya rika yi masa wasu tambayoyi. Da ya ga haka, sai ya yi sauri ya bar wurin.
Femi Fani-Kayode Ya Nemi A Kore Ni Daga Aiki:
Charles ya ce daga baya tsohon ministan ya kira Editan Daily Trust, ya nemi a kore shi.
Kakakin gwamnan Cross River, Ita, ya ce tambayar rainin hankali aka yi wa Femi, shi ya sa ya harzuka.
Charles ya ce ya yi nadamar hakurin da ya ba Femi Fani-Kayode.
“Shekaru na 53 a duniya. Bai girme ni sosai ba fa. Kuma ni ma ina da iyali. Da na sani da ban ba shi hakuri ba.”
Discussion about this post