Da shugabannin addinai na fadi wa mabiyansu gaskiya da ba za a rika samun tashin hankali ba – Zailani

0

Kakakin majalisar dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Zailani ya gargadi shugabannin addinai da su rika fadi wa mabiyan su gaskiya komai dacinta maimakon zuga mabiyansu a wuararen ibada da tallata kiyyayya.

Zailani ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a dakin taro na fadar gwamnatin Kaduna a lokacin da gwamnatin jihar ke karbar bakoncin shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya da suka ziyarci Kaduna a makon jiya.

Zailani ya kara da cewa ” Gaskiya ce ba a so a rika fadi, idan kaje wasu wuraren ibadan sai kaji masu jagoran su na zuga su sannan suna tallata musu kiyyar abokan zaman su da ba addinin su daya ba. Hakan shine yake ruruta fitina a tsakanin mutane.

A karshe ya ce dole sai an dawo an hada kai sannan shugabannin addinai na karantar da mabiya sakon Allah madaukakin sarki kamar yadda yazo a littafan addinan mu, ba za a samu zaman lafiya ba.

Haka shima sanatan dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Uba Sani da ya halarci wannan taro ya roki wadanda ba mazauna garin Kaduna bane da su rika tauna kalaman su kafin su furta su.

” Wannan rikici ya shekara sama da 40 anan fama da shi. A karon farko an samu gwamna jarumi da ya lashi takobin sai an kawo karshen wannan matsala. Amma kuma saboda yadda wasu ke karkata labarin ainihin abinda ke faruwa, mutane da yawa bangare daya kawai suke ji banda wasu bangarorin.

Share.

game da Author