Tattalin Arzikin Cikin Gida na Najeriya (GDP) ta kakare tare da yin tafiyar-kura, abin da aka fi sani da ci gaban mai ginin rijiya, a tsakanin watannin Afrilu, Mayu da Yuni na shekarar 2020.
Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), mallakar gwamnatin tarayya ce ta bayyana haka a ranar Litinin.
Rahoton Bayanan Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) na watannin Afrilu, Mayu da Yuni (Q2 2020), ya nuna cewa saboda tsayawa cak da harkokin cinikayyar kasa da kasa da zirga-zirgar cikin kasashe a lokacin zaman gida tilas saboda cutar Coronavirus, tsakanin Afrilu zuwa karshen Yuni, tattalin arzikin ya shiga jula-jula.
An dai rufe hada-hadar komai da komai a kasashen duniya saboda barkewar annobar Korona a cikin watannin uku.
Najeriya ta kulle komai da komai, tun daga harkokin gwamnatin tarayya, makarantu, kasuwanci, zirga-zirga, masallatai da coci-coci saboda Coronavirus.
NBS ta lura a ranar Litinin cewa wadancan tsauraran matakan da aka gindaya na hana zirga-zirga ne suka haddasa tattalin arzikin gida na Najeriya ya rika yin tukin baya-da-baya.
Wannan jula-jula da tattalin arziki yw shiga, ya kawo karshen bunkasar da ake gani ya dan yi cikin shekaru uku,tun bayan kuncin tattalin arzikin da Najeriya ta shiga cikin 2016.
PREMIUM TIMES ta buga labari a cikin makon da ya gabata cewa sama da mutum milyan 50 a Najeriya ba su day cin yau balle na gobe.
A karshen makon nan kuma jaridar Punch ta buga labarin cewa kashi 61 zuwa 63 bisa 100 na ‘yan Najeriya a sayen abincin yau da gobe ‘yan kudaden da suke samu ke tafiya.