Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 321 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –98, FCT-34, Kaduna-30, Nasarawa-25, Benue-21, Filato-17, Rivers-15, Adamawa-11, Ogun-11, Enugu-9, Edo-8, Delta-7, Ekiti-7, Gombe-5, Ebonyi-4, Bayelsa-3, Kano-3, Ondo-3, Cross River-2, Imo-2, Kebbi-2, Niger-2, Abia-1, Bauchi-1
Yanzu mutum 52,548 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 39,257 sun warke, 1004 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,287 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 17,992 FCT –5,028, Oyo – 3,050, Edo –2,545, Delta –1,708, Rivers 2,063, Kano –1,711, Ogun – 1,625, Kaduna –2,041 Katsina –771, Ondo –1,515, Borno –740, Gombe – 714, Bauchi – 644, Ebonyi – 964, Filato -2,135, Enugu – 1,052, Abia – 750, Imo – 523, Jigawa – 322, Kwara – 936, Bayelsa – 373, Nasarawa – 421 , Osun – 768, Sokoto – 156, Niger – 239, Akwa Ibom – 271, Benue – 451, Adamawa – 217, Anambra – 194, Kebbi – 92, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 225, Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.
Gwamnati zata siyo na’urorin gwajin KORONA na naira biliyan 8.49
Ganin yadda cutar Korona ke dada yaduwa a kasar nan gwamnati ta ware naira biliyan 8.49 domin siyo kayan yin gwajin cutar a kasar nan.
A jawabin da ministan kiwon lafiya Osagie Ehinare yayi a wajen taron majalisar zartaswa ta Kasa ranar laraba, ya ce hakan ya zama dole ganin yadda cutar ke dada yaduwa a Najeriya.
Ya ce siyo wadannan na’urori zai taimaka wajen aikin dakile yaduwar annobar Korona a duniya.
Osagie ya ce hukumar NCDC za ta bude sabbin wurare yin gwajin Korona a duk kananan hukumomin dake kasar nan domin dakile yaduwar cutar.
Discussion about this post