CIYAR DA DALIBAI LOKACIN KORONA: Naira milyan 538 muka kashe ba naira bilyan 13 ba -Minista Sadiya

0

Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bada cikakken karin haske dangane da ji-ta-ji-ta da labaran bogi da ta ce ake yadawa kan adadin kudaden da ake kashewa a kullum a Shirin Ciyar da Dalibai Daga Gida.

Ministar ta yi wannan karin haske ne a ranar Litinin, lokacin da ta ke bayani a taron Kwamitin Shugaban Kasa, a Abuja.

Ta ce: “Ana ta watsa ji-ta-ji-ta da karairayi a kan daya daga cikin bangarorin tallafin da wannan ma’aikatar ke bayarwa, wato Shirin Ciyar da Dalibai Daga Gida, wanda aka aiwatar a jihohi uku, bisa umarnin da Shugaban Kasa ya bayar tun a ranar 29 ga Maris, 2920.

“Wannan shiri na ciyar da dalibai daga gida a lokacin zaman gida sakamakon barkewar cutar korona, ba shiri ne da wannan ma’ikata ita kadai ta kirkiro ba.”

Sadiya ta kara da cewa kafin a aiwatar da shirin, sai da ma’aikatar ta ta tuntubi daukacin gwamnonin kasar nan, su su ka bada shawarar cewa Ciyar Da Dalibai Daga Gida a lokacin shi ne hanyar mafi dacewa a lokacin zaman kullen korona a gida.

“Daga nan kuma masu ruwa da tsaki a harkar su ka amince a fara da FCT Abuja, Legas da Jihar Ogun a matsayin jihohin da za a yi gwajin shirin.”

Yadda aka amince a raba N4,200 a gidaje – Sadiya

Ta ce: “An amince cewa za a raba wa kowane gidan da ke cikin lissafi N4,200. Kuma ba haka kawai aka kintaci adadin kudaden aka rubuta ba.

“An yi amfani da kididdigar alkaluman kiyasin yawan iyalin da ke kowane gida da Hukumar Kididdigar Alkaluma ta Kasa (NBS) da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) su ka yi, cewa akalla kowane gida a dauka akwai mutum 5 zuwa 6 a ciki. A cikin su shida din kuma kididdigar ta kiyasta akwai cima-zaune mutum 3.

“Saboda haka sai mu ka yi amfani da tsohuwar kididdigar da ke kasa ta Ciyar da Dalibai daga Gida, wadda ake bai wa kowane dalibi abinci kyauta sau daya a rana. Abincin kowane yaro na daidai da N70 ne. Idan ka dauki kwanaki 20 da ake zuwa makaranta a wata daya, to yaro daya zai ci abincin N1,400 kenan a wata. Cikin wata 3 yaro ya ci abincin N4,200 kenan. To kun ji yadda aka bi diddigin kaiwa ga adadin kudaden da aka kashe a kowane gidan da ya amfana da shirin.”

“A FCT, Legas Da Ogun Kadai Aka Kaddamar Da Shirin”

Minista Sadiya ta bayyana cewa wannan shiri an kaddamar da shi ne a FCT Abuja, Jihar Legas da Jihar Ogun kadai.

“A yankin FCT Abuja, an shiga garuruwa aka raba wa gidaje 29, 609, a Jihar Legas gidaje 37,589 su ka ci moriyar shirin. A Jihar Ogun kuma gidaje 69,391 su ka amfana.

“Baki daya jimillar gidaje 124,589 kenan su ka ci moriyar shirin ciyarwar da aka kaddamar tsakanin ranakun 14 ga Mayu zuwa 6 ga Yuli, 2020. Kenan gaba daya adadin kudaden za su kama N523,273,800.

“Kuma a kula cewa ba fa a kullum ne aka rika kashe wadannan kudaden ba. An fara kaddamar da na FCT Abuja, sai na Legas, daga nan kuma sai na Ogun.”

Ministar ta ce babu inda ta taba cewa an raba wa kowane gida a kasar nan kudade ko kayan tallafi. Ta ce amma dai an raba wa kowace gwamnatin jiha ta karbi nata tallafin da aka ce ta raba wa marasa galihu da mabukata a jihohin su.

Share.

game da Author