Gwamnatin Tarayya ta fara binciken manyan kantinan sayar da magunguna, wadanda suka tsawwala farashin Hydroxychloroquine, maganin zazzabin nan da aka rika rade-radin ya na warkar da cutar Coronavirus.
Wadansu manyan kantinan sayar da magunguna sun rika tsawwala wa kwalin kwayoyin maganin kudi, daga naira 3,000 zuwa naira 50,000 har abin da ya yi sama.
Wani kwalin maganin da aka buga a shafukan soshiyal midiya, mallakar Ebus Pharmacy da ke garin Fatakwal, an buga farashin maganin na Hydroxychloroquine naira 50,000 maimakon naira 3,000 da aka sani ana sayar da maganin.
Mai kantin sayar da maganin na Ebus Pharmacy da ke Fatakwal, mai suna Boniface Ebugosi, ya bayyana cewa daga kasar waje ya sayo maganin da tsada, saboda tashin-gwauron-zabon da dala ta yi, ita kuma naira darajar ta ta kara sakwarkwacewa.
An samu wasu manyan kantinan sayar da magani a Fatakwal su na sayarwa naira 50,000 abin da ya yi sama.
An fara tsawwala wa Hydrocodone kudi ne bayan fitar wani bidiyo da wata mazaunar Amurka, ‘yar Kamaru da ta yi karatu a Najeriya, ta ce ta rika yin amfani da Hydroxychloroquine ta na warkar da masu cutar Coronavirus a asibitin da ta ke aiki a Amurka.
Hukumar Tabbatar da Farashin Kayyyaki ta Kasa, (FCCPC) ta bayyana cewa sun kai samamen tabbatar da yadda wasu manyan kantina suka rika tsawwala farashin Hydroxychloroquine.
Shugaban Hukumar Babatunde Inukera, ya ce, “Mun kai samame Ebus and Avis Pharmacy a Fatakwal, mun kai a HealthPlus a kantinan su na Lagos da Abuja, kuma mun kai a Tonia Pharmacy, H-Medix da New Health a Abuja.”
Babatunde ya ci gaba da bayyana irin yadda aka kama wadannan manyan kantinan su na sayar da maganin zazzabin Hydroxychloroquine da tsadar gaske.
“New Health na sayarwa daga naira 50,000 zuwa naira 65,000. A HealthPlus mun samu Hydroxychloroquine kala biyu – akwai wanda suke sayarwa naira 33,000, sannan kuma akwai dan naira 75,000 a farashin su.”
Ya ce sun kuma binciki wasu magungunan da ake bai wa masu cutar Coronavirus, inda suka gano cewa duk an tsawwala farashin su zuwa kashi 66% bisa 100%, har ma 89% bisa 100%.
Ya ce tuni an gudanar da wasu masu manyan kantinan sayar da magunguna a kan irin wannan tsawwala farashin da ya ce haramtacce ne, zalunci ne da kuma rashin rashin tausayi.