TSARO: ‘Na gamsu da ayyukan samar da tsaro da kuke yi, kuna iya kokarin ku’ – Buhari ga Manyan Hafsoshin Najeriya

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa manyan hafsoshin dakarun Najeriya bisa hubbasan da suke yi wajen ganin an kawo karshen ta’addanci a Kasar nan.

Bayan ganawa da shugaba Buhari yayi da manyan hafsoshin dakarun Najeriya a fadar shugaban kasa, tare da mai bashi shawara kan harkar tsaro, Buhari ya bayyana cewa tabbas wadannan hafsoshi sun cancanci a yaba musu bisa ayyukan samar da tsaro da suke yi a Najeriya, sai dai kuma yace dole a sa himma wajen ganin an gama da burbudin wadanda suka rage kwata-kwata a Najeriya.

Mai ba shugaba Buhari Shawara akan harkar tsaro, Babagana Monguno, ya shaida wa manema labarai cewa Buhari ya gamsu da yadda manyan jami’an tsaron kasa ke gudanar da ayyukan su na samar da tsaro a Najeriya.

Monguno ya ce ” Shugaba Buhari ya yaba da ayyukan samar da tsaro da manyan hafsoshin ke yi a kasar nan inda yace ” Ni dai na gamsu da ayyukan su kuma ina yaba musu.” Inji Buhari.

” Abinda yafi damu na shine alkawuran da muka dauka wa mutanen Najeriya cewa zamu samar musu da tsaro. Na ba da odar a yi wa kakkyawar fannin tsaron kasar nan garambawul sannan ya umarci manyan hafsoshin Najeriya su canja salon yaki da suke amfani da shi.

” Dole a canja salon yaki, da salon yadda ake aikin samar da tsaro a kasar nan.

Monguno ya ce wannan shine karo na uku da ake zaman kwamitin tsaro na kasa a fadar shugaban kasa.

A zaman kwamitin na yau, an maida hankali kan yadda safara da ta’ammali da ake yi da muggan kwayoyi ya zama ruwan dare a kasar nan, musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Da Kuma tsara yadda za a tunkari wannan matsala.

Share.

game da Author