Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabinmu Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki dayansu. Bayan haka:
Ya ku jama’ah, wato sau da yawa ban fiye yin magana akan wasu abubuwan ba, domin ba komai ne zaka mayar wa da mutane amsa akai ba, saboda mun san cewa wallahi wasu mutanen basu ma isa a mayar masu da martani ba. Kawai wani lokacin mukan yi magana ne domin yin shirun zai sa mutanen da basu san me yake faruwa ba, ba zasu fahimci gaskiyar al’amari ba, sai ayi masu karya, su dauka cewa karyar ita ce gaskiya, alhali kuwa sam ba haka ba ne. Kuma mu mun daukar wa kan mu alkawarin bayyanawa duniya gaskiya tsakanin mu da Allah, ba tare da jin tsoron zargin duk wani mai zargi ba.
Jama’ah, idan mafadin magana wawa ne, ai majiyinta ba zai zama wawa ba, ko akasin haka. Musamman a daidai wannnan lokacin, amma dai yana da kyau mutane su rinka fuskantar abubuwa da idon basirah da kuma dogon nazari akan irin abubuwan da suke faruwa a tsakaninsu.

A lokacin da Allah cikin ikon sa da kaddarawarsa ya bawa Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll Sarautar Kano, yazo ya tarar da rigingimu kala-kala, iri-iri, masu tarin yawa, wadanda cikin ikon Allah, saboda iliminsa da hikimarsa, da basirarsa da hangen nesansa, Allah ya taimake shi yayi iya kokarinsa don ganin ya warware iya abinda Allah ya bashi Ikon warwarewa. Kama daga bangaren Sarauta da ma abinda ya shafi sha’anin yau da kullum.
Sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta, wadda Alhaji Aminu Babba Dan Agundi yake kan ta, tana cikin irin rigingimun da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi ll ya tarar, wadda kuma alhamdulillahi, Mai Martaba Sarki yayi rawar gani don bin duk wasu hanyoyin da suka dace, na ganin bai kwayewa wanda ya gada, wato babansa, tsohon Sarki baya ba, akan irin hukuncin da ya yanke na yin awon gaba da rawanin Aminu Babba Dan Agundi din. Sarki Sanusi ya tabbatar da hukuncin da Sarki Ado ya yanke domin ya kare masa mutuncinsa da Martabarsa. Duk duniya ta san anyi haka.
Aminu Babba Dan Agundi yayi kokarin shiga jikin Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi ll, don ganin burinsa ya cika na dawo masa da Sarautarsa, wadda marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya warwareta, amma a lokacin, Sarki Sanusi ya tabbatar masa da hakan ba zai taba yiwuwa ba, domin hukunci ne da Magabata suka yanke, wanda shi kuma ba zai warware shi ba. Bayan da yaga wannnan damar ba ta samu ba, sai yabi hanyoyin yin Shari’ah da Masarauta, wato zuwa kotu. Da ma tun tsohon Sarkin yana raye yake ta gurfanar dashi gaban Shari’ah, duk duniya ta shaida an yi haka.
Aminu Babba Dan Agundi yaci nasara a kotu, ya kayar da Masarauta a kotun farko ta Kano (wato High court) da kotu ta biyu, wato kotun daukaka kara kenan (Appeal court), wannan ya faru ne lokacin marigayi Sarki Ado, Allah ya jikansa da rahama, amin.
Da Allah ya kawo Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II sai yasa a daukaka kara zuwa kotun koli, ya canza lauyoyi kwararru wadanda za su wakilci masarauta, shine kotun koli tayi watsi da hukunce-hukuncen da aka yi a kotunan kasa, kotun koli ta ce abinda Sarki Ado yayi daidai ne, na sauke rawanin Aminu Babba Dan Agundi.
In dai takaita maku bayani, haka suka yi ta bugawa da Mai Martaba Sarki Sanusi II, kuma shi yasan cewa fadan yafi karfin sa. Shari’ah ta kai su har kotun koli, kuma kotun kolin kamar yadda na fada, ita ma dai kwanan nan ta tabbatar da wancan kuduri na marigayi Sarki Ado, wanda Sarki Sanusi II yace shi ba zai sauka akai ba, domin yin hakan tamkar yaye wa Sarki Ado zane ne a kasuwa! Duk duniya ta shaida hukuncin da kotun kolin ta yanke, domin na san har wasu daga cikin ku ma sun ga takardun hukuncin da aka yanke.
To a kwana a tashi, dama Malam bahaushe yace da dan gari akan ci gari. Kuma da ma ance naka-ke-bada-kai, kwatsam wata matsala ta zo ta sabani tsakanin Gwamnatin jihar Kano da Mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi ll a wancan lokaci kenan, kuma kamar yadda duniya ta shaida, wannan rikici ya faru ne saboda gaskiyar da Mai Martaba yake akai, kuma yake fada masu, su kuma mutane ne wadanda basu son gaskiya, kuma suna adawa da ita.
Abubuwa sun faru marasa dadi, wanda shi Gwamnan jiha, a wancan lokacin ya samu hadin kan wasu daga cikin ‘yan uwan Mai Martaba Sarki Sanusi, kuma zuri’ar gidan Dabo, wadanda suke hassadar Sarki saboda baiwa da Allah yayi masa, wannan ya jawo Ganduje yayi abinda yayi, kamar yadda kuka sani.
Kowa ya sani, Aminu Babba Dan Agundi ya taka muhimmiyar rawa wurin fada da Sarki Sanusi, ya basu goyon baya dari-bisa-dari, da shi aka yi duk abunda suka yi, ba don komai ba, sai don ganin cewa burinsa ya cika, na dawowarsa kan Sarautarsa.
Yabi duk hanyoyin da yake ganin zai bi don yayi nasara, ya hada kai da Gwamnati, ya hada kai da duk wani wanda yasan cewa yana hassadar Sarki Sanusi. Domin wallahi da kan su, suna fadar irin gudunmawa da hadin kai da ya basu wurin cimma burin su, har dai abinda Allah ya kaddara zai faru yazo ya faru.
Kuma majiya mai tushe ta tabbatar da cewa da ma bai yi masu aikin ba sai da sharadin cewa za’a dawo da shi cikin Masarautar Kano. To bayan kura ta lafa ne, sai ya dawo da maganarsa, tare da neman a cika masa alkawarinsa. To da ma fa ‘ya’yan Baba ne, Gwamna ya basu umurnin a cika masa alkawarinsa, saboda gudummawar da ya basu wurin yaki da Sarki Sanusi II, duk da kotu ta yanke hukunci akai. Dama kuma kun san halin wasu ‘yan siyasar, basu mai da doka komai ba, duniya tana kallon su suka yi watsi da hukuncin kotu.
Kuma su basu isa suyi musun maganar Gwamna ba, na umurnin da ya basu na dawowa da Aminu Babba Dan Agundi kan Sarautarsa, tun da dama su Sarakunansa ne ba na jama’ah ba. Nan take suka amince da dawo masa da Sarautar. Wanda kuma yin hakan, sabawa ne tare da warware alkawari, da hukuncin da Mahaifinsu yayi. Kun ga anan, sai duniya ta kara shaida cewa, lallai albasa ba tayi halin ruwa ba ke nan!
Kuma ‘yan uwana masu daraja, abu ne da kowa ya sani, cewa Aminu Babba Dan Agundi tun da marigayi Sarki Ado ya cire shi daga sarauta, shekara sama da goma, har Allah yayi wa Sarki Ado rasuwa, yawo yake yi yana zagin sa, yana cin mutuncinsa. Alhali Sarki Ado shine ya nada mahaifinsa, wato Babba Dan Agundi Sarkin Dawaki Mai Tuta, ba tare da ya gaje ta ba. Kuma tun mahaifinsa Babba Dan Agundi yana da rai, marigayi Sarki Ado ya nada dan nasa Aminu, kuma ya ba shi ‘yarsa ya aura, daga baya yayi mata wulakanci, ya sake ta. Sannan kuma ya nuna wa Sarki Ado rashin da’a da ladabi, aka cire shi daga sarautar. Ko kotun koli ma ta tabbatar da cewa rashin ladabin da yayi shi yasa aka cire shi, kuma Sarki Ado yayi daidai.
Jama’ah ku sani, Gwamna Ganduje ma ya dade yana tursasawa Sarki Muhammadu Sanusi II lamba, akan wai ya mayar da Aminu Babba Dan Agundi kan kujerarsa ta sarauta, amma Sarki Sanusi yace ba zai yi ba saboda irin abinda yayi wa Sarki Ado na cin mutunci da rashin da’a, amma wai yau, ga wanda yake da’awar cewa wai shi dan Sarki Ado ne, ya kasa kare masa mutuncinsa da martabarsa, ya mayar da Aminu Babba Dan Agundi sarautar da yasan mahaifinsa Sarki Ado ya cire shi. Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!
Duk da cewa lauyoyin Sarki Muhammadu Sanusi II sun samu nasara a kotun koli, yau Aminu Ado yayi biris da wannan hukuncin, ya shafawa mahaifinsa Sarki Ado Bayero toka a fuska, ya karrama makiyinsa, ya mutunta wanda bai san girmansa ba.
Allahu Akbar! Wallahi dadin abun duk zamu mutu, mu koma ga Allah yayi hukunci!
Allah ya sawwake, Allah yasa mu gama lafiya da magabatanmu, kuma duk abun da zai sa muci mutuncin magabatanmu, ya Allah kar ka sa mu aikata shi, amin.
Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.