Dakataccen Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya sake rubuta wa Shugaban Kwamitin Bincike Ayo Salami wasika, ya na karyata zargin danganta shi da wawurar makudan kudade, har ana barbada a shi a kafafen yada labarai a lokacin da ya ke tsare.
Magu ya rubuta wasikar ta hannun lauyan sa Wahab Shittu, kuma ya zargi kwamitin binciken da kin ba shi isasshen lokaci domin shirya kare kan sa.
Cikin wasikar da Magu ya aika a ranar Laraba, ya nuna cewa har yau Kwamitin Bincike a karkashin Ayo Salami bai aika masa da sammacin irin korafe-korafen zargin da ake masa ba.
Har yau kuma Magu ya ce ba a aika masa da kwafen rahoton Kwamitin Shugaban Kasa mai Binciken Adadin Kudin Da Dukiyar Da EFCC ta Kwato ba.
Kwamitin mai suna PCARA, Shugaba Muhammadu Buhari ne ys kafa shi a cikin 2015, kuma ya mika rahoton sa a cikin 2018.
Sai dai kuma har yau babu wanda ya san sakamakon binciken da kwamitin wanda Buhari ya kafa ya binciko.
Sai fa yanzu da batun zargin Magu ya taso ne aka fara ganin jaridu na fallasa wasu batutuwan salwantar kudade da ake zargin Magu da su.
Tuggu, Kage Da Kitimirmira Aka Shirya Min -Magu
“Don haka ni dai game da bayanan da na yi a sama, har yau ba a bai wa wanda muke karewa isasshen lokacin da zai kare kan sa ba. Kuma har yau ba ku aiko masa da kwafen zarge-zargen da ake yi masa ba.
“Tuhume-ruhumen da ku ke wa wanda mu ke karewa, duk karya ce, shiri ne, tuggu ne, kage ne da kitimirmirar bata masa suna, zubar masa da kima da kuma lalata martabar Hukumar EFCC baki daya. Wadda wannan hukuma ta yi matukar tasiri sosai a zamanin da wanda mu ke karewa ke jagorantar hukumar.
Takardar dai ta yi bayanan yadda aka zargi Magu da bai wa Mataimakin Shugaban Kasa naira bilyan 4. Kuma shi Yemi Osinbajo din ya karyata.
Sannan kuma an zarge shi da tura masu bincike gidan tsohon Shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalam Abubakar da kuma gidan T.Y Danjuma. Su ma duk sun fito sun karyata.
Daga karshe dai lauyan Magu ya ce idan dai bincike ake so a yi cikin adalci, to a bai wa Magu ‘yancin kare kan sa, ba wai a ci gaba da yi masa bi-ta-da-kulli ba, wato dukan-kabarin-kishiya.