HARKALLAR NDDC: ‘Yanzu ne ma zan yi fallasa, a saurare ni – Nunieh, tsohuwar shugabar NDDC

0

Tsohuwar shugabar Hukumar NDDC, hukumar nan ta raya yankin Neja-Delta, wadda kwamacalar zargin jidar bilyoyin kudade ta dabaibaye, ta bayyana cewa za ta kara zunguro gidan rina da zirnako ta kara fallasa yadda aka rika jida da lodin makudan kudade a hukumar.

Joi Nunieh ta yi wannan barazanar mintina kadan a yau Laraba bayan da Gwamna Nyesom Wike ya ceto ta daga cikin gidan ta, inda tun da farko jami’an ‘yan sanda suka yi wa gidan zobe.

Gungun ‘yan sanda dauke da manyan bindigogi suka kewaye gidan Nunieh tun wajen karfe 4 na asubahin yau Alhamis.

Amma daga baya wani bidiyo da aka rika watsawa a soshiyal midiya, ya nuna yadda gwamna Wike ya ja zugar jama’a har gidan ta, ya tafi da ita cikin gidan Gwamnatin Jihar Fatakwal.

Da ta ke bayani a cikin gidan gwamnatin, Nunieh ta ce Ministan Harkokin Neja-Delta ne, Godswill Akpabio ya turo ‘yan sanda su kewaye gidan ta.

A yau ne ya kamata ta sake bayyana a gaban Kwamitin Bincike na Majalisar Tarayya, inda a makon jiya ta je ta yi fallasa, kuma daga bisani ta kara yin wata fallasar a gidan talbijin na Arise TV.

“Ina jin shi Akpabio kokari ya yi domin ya hana ni bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa, domin ya na tsoron idan ba fito da nawa ba’asin, to zai tsure sosai.” Inji Nunieh.

“A yau dai ya yi nasara, amma na san Majalisa za ta kara ware wata ranar da za ta gayyace ni domin na bayar da nawa ba’asin.

Akpabio Ya Nemi Ya Kashe Ni:

“Akpabio ya nemi ya kashe ni tabbas. Amma dai ba zai iya ba. Domin ni ba daga Uyo na ke ba. Amma me ya sa mutane ke runanin Akpabio gogarman dan sara-suka ne?”

“Mutumin da ya nemi yin lalata da ni a gidan sa. Mutumin da ya saci makudan kudade amma ya na gida abin sa a zaune. Mutumin da ya sace fayil-fayil na bayanan kudaden gwamnari, ya na gida zaune. Mutumin da ya nemi na yi rantsuwar ‘yan kungiyar asiri don kada na fallasa shi, ya na gida zaune.” Inji Nunieh, kuma ta na nufin Akoabio.

Da PREMIUM TIMES ta tunrubi kakakin Akpabio, sai ya ce ai jami’an ‘yan sanda ne ya kanata su yi magana, ba shi ba.

Share.

game da Author