Yayin da ake tsakiyar sukar matsayar da gwamnatin tarayya ta dauka cewa dalibai masu fita sakandare a 2020 ba za su rubuta jarabawar WASSCE a 2020 saboda annobar Coronavirus ba, gwamnati kuma a na ta bangare na ci gaab da kare dalilai da hujjojin ta na kin barin dalibai a Najeriya su rubuta jarabawar ta fita sakandare.
Cikin makon jiya PREMIUM TIMES ta buga labarin da gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a bana dalibai ‘yan ajin karshe na sakandare ba za su zauna jarabawar ba, saboda barkewar cutar Coronavirus.
Cikin wadanda suka fara sukar wannan matsaya da kakkausan harshe, har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma shugaban masu adawa.
Majalisar Tarayya ita ma ta soki lamarin, ta ce kamata ya yi gwamnati ta sake tunani.
Atiku ya ce hana dalibai rubuta jarabawar WASCE a 2020 gurguwar dabara ce.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce rashin dabara ce da gwamnatin tarayya ta soke zaman jarabawar da daliban shekarar karshe na sakandare za su yi ta WASCE.
Gwamnati ta soke zaman jarabawar da a baya ta ce za a yi tsakanin 5 Ga Agusta zuwa 5 Ga Satumba, ta dawo ta ce bana kwata-kwata daliban Najeriya ba za su rubuta WASSCE a 2020 ba.
Jarabawar wadda Hukumar Shirya Jarabawar Afrika ta Yamma (WAEC) ke shiryawa, tun farko gwamnatin ta dakatar da ita a watan Afrilu, wata days kafin fara jarabawar a cikin Mayu.
An dage zaman jarabawar saboda annobar Coronavirus, wadda ya zuwa yanzu sama da mutum 30,000 suka kamu a Najeriya, yayin da ta kashe sama da mutum 77.
“Matakin da gwamnati ta dauka na soke jarabawar WASSCE a 2020, dabarar-rashin-,dabara ce. Danyen hukunci ne, wanda a gaba zai tsame wa tsarin samar da ilmi wata kurwa a kasar nan da za ta rika addabar ilmi a kasar nan.”
Ya ce wani koma-baya ne ga matasan Najeriya milyan 1.5 da ke rubuta jarabawar WASSCE a duk shekara a Najeriya.
“Ka hana matasa masu wannan dimbin yawa rubuta jarabawa tsawon shekara daya, ka maida su baya, ta yadda na sauran kasashen duniya za su tsere musu fintikau. Ga shi kuma dan tallafin da kasashe ko hukumomi da kungiyoyin waje ke bayarwa a kan ilmi, sun dogara ne ga yadda ci gaban ilmi a kasar ke bunkasa.”
Da ya ke kawo mafita, Atiku ya ce WASSCE za ya iya shirya zaman jarabawar ta yadda yadda za a tsitstsinka daliban, ba sai an gwamutsa su a wuri daya ba, ki kuma ba sai an zauna jarabawar darasi daya a rana daya dungurugum ba.
Dimbin jama’a na ta sukar matsayar da gwamnatin tarayya ta dauka, har ana ta rubuce-rubuce cewa matukar za a hana dalibai zauna jarabawar fita sakandare wato WASSCE, to bai kamata kuma gwamnati ta gudanar da zaben gwamna a jihohin Edo cikin Satumba da Ondo cikin Oktoba ba.
Sai dai kuma gwamnati ta kara jaddada cewa har yanzu ta na nan a kan bakan ta, amma dai duk da hakan ta na ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a lamarin.
Haka dai Karamin Ministan Ilmi, Chukwuemeka Nwajuiba ya shaida wa manema labarai bayan kammala Taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba, a Fadar Shugaban Kasa.
Ya ce matsayar da Ministan Ilmi Adamu Adamu ya dauka, ta yi daidai da sharudda, ka’idoji da shawarwarin da Hukuma Dakile Coronavirus ta Kasa ta gindaya.
Ya ce duk da su na kan tuntubar masu hannu a batun jarabawar, har yanzu dai gwamnati n kan bakan ta tukunna.
Discussion about this post