Lokacin da tsohon Shugaban EFCC, Nuhu Ribadu ya samu sabani da masu rike da madafun ikon Najeriya, an matsa masa lambar da ta kai ga an cire shi a cikin Disamba, 2007.
An raba Ribadu da shugabancin EFCC saboda ya yi kokarin gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori, wanda a lokacin ya na daga sahun gaban na hannun daman tsohon Shugaban Kasa marigayi Umaru ‘Yar’adua.
Bayan wasu ‘yan shekaru da cire Ribadu, ya ja hankalin kafafen yada labarai, har dai ya kai ga ya fito ya fallasa bahallatsar da ta rika gudana a lokacin.
Daga cikin wadanda Ribadu ya lissafa sun gurgunta kokarin EFCC, akwai Minstan Shari’a na lokacin, Micheal Aondoakaa, wanda ya rika kitsa makarkashiyar tabbatar da cewa EFC. ba ta yi nasara ba.
“A matsayin Andoakaa na Ministan Shari’a, sai ya kasance ba shi da wani aiki a kasar kacokan sai kulla kullalliyar hana EFCC gudanar da aikin ta. Ya rika amfani da irin su Farfesa Ben Nwabueze, tsohon lauya su na yi wa EFCC muguwar farfagandar zubar wa hukumar EFCC da martaba.”
Ribadu ya ce Ministan Shari’a na lokacin din ya samu kwarya daidai burmin sa, ys hada kai da ita, wato Farida Waziri, wadda ita ce ta maye gurbin Ribadu din.
Ribadu ya kara da cewa “Farida Waziri ta yi wa EFCC mummunan lahanin da har yau ya na doyin da kudaje ba su daina hawa kan sa ba.”
Yayin da Farida a lokacin ta musanta abin da ya fada a kan ta, shi kuwa Minista Andoakaa bai yi wani raddi ba.
Ribadu ya yi kokarin gurfanar da manyan kasar nan, ciki kuwa har da ogan sa a lokacin, kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tafa Balogun, wanda aka samu bargar motoci rubutu a cikin gidan sa.
Cikin 2007 Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Mike Okiro ya cire Ribadu daga shugabancin EFCC, kuma aka tura shi yin kwas na shekara daya a Cibiyar Koyon Dabaru da Tsare-tsaren Mulki da ke Kuru, Jos, Jihar Filato.
Bayan shekara daya sai Hukumar Kula da Aikin ‘Yan Sanda ta Kasa ta sallami Ribadu daga aikin dan sanda kwata-kwata.
An cire Ribadu cikin 2008, aka cire Farida Waziri cikin 2011, shi kuma Lamorde cikin 2015 sai kuma Ibrahim Magu cikin 2019.
Masu lura da al’amurran kuwa na dora laifin yawan korar kowane Shugaban EFCC a kan masu yunkuri da makarkashiyar hana yaki da cin hanci a Najeriya.
Yayin da Farida Waziri ta rika shan fama da Ministan Shari’a Adoke Mohammed a lokacin ta, ya rika kokarin kashe karimtsa da rimatson shari’un wasu karta-kartan da suka wawuri dukiyar Najeriya.
Babu wani takun-saka da ya wakana tsakanin Adoke da Lamorde. Idan ma har akwai, to bai fito fili ba, kamar yadda yadda yadda fito a yanzu tsakanin Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ibrahim Magu, har ta kai sun sun yi kare-jini-biri-biri jini a cikin jaridu.
Masana da masu sharhi da dama sun tofa albarkacin bakin su, kowa na bayyana yadda irin wannan kakuduba ke faruwa ta na rage kima da martabar gagarimin aikin yaki da masu wawura da satar kudaden gwamnati da kuma ayyukan zambar kudade a Najeriya.