BABBAN SALLAH: Mutanen Abuja su yi Sallar Idi a masallatan Juma’a dake kusa da su – Minista

0

Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya yi kira ga zauna garin Abuja da su yi Sallar idi a masallatan Juma’a dake kusa da su maimakon su dunguma zuwa filin idi.

Bello ya fadi haka ne a wani takarda da babban sakataren yada labaran ma’aikatar sa Anthony Ogunleye ya raba wa manema labarai ranar Talata a Abuja.

Ya ce masallata su garzaya masallatan dake kusa da su ne su yi sallar Idi maimakon zuwa filin idi.

Bello ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne bayan ta tattauna da kungiyar mamalai kan tsarin hanyoyin da za su taimaka wajen kare kiwon lafiyar mutane daga kamuwa da cutar Korona a lokacin shagulgulan babbar Sallah.

Bayan haka Bello ya yi Kira ga malamai da su tsara hanyoyin da zai taimaka wajen hana cinkoso a masallatai. Sannan kada a wuce awa daya a wajen Sallah.

Gwamantin Tarayya ta bada da ranakun Alhamis 30 ga Yuli da ranar Juma’a, 31 ga Yuli ranakun hutun Babbar Sallah sannan kuma ta yi ga ‘Yan Najeriya su kiyaye dokoki da sharuddan gujewa kamuwa da cutar Korona da gwamnati da hukumar NCDC ta gindaya a lokacin shagulgular Babban Sallah.

Ana sa ran za a yi sallar Idi ranar Juma’a.

Abuja nma daga cikin wuraren da ake samun karuwar wadanda suka kamu da Korona a Najeriya.

Share.

game da Author