Balbalin Gobara ta yi ajalin mutum daya a jihar Kano

0

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutum daya ya rasu a gobarar da aka yi a Kofar Ruwa dake karamar hukumar Dala ranar Litini.

Kakakin hukumar Saidu Mohammed ya ce wannan ibtila’i ya faru a daren Litini inda tanki dankare da man fetir ya Kama da wuta a gidan man Audu Manager.

” Da misalin karfe 10:30 na dare wani Bello Musa ya kira hukumar mu yana bayanin cewa gobara a Kofar Ruwa.

“Nan da nan ma’aikatan mu suka gaggauta garzayawa wannan wuri. Isar su ke da wuya jami’ai suka yi kokarin kashe wutar sai dai kash, wani mai suna Adamu Salisu ya rasu a wannan gobara.

Idan ba a manta ba a watan Afrilu ne bukkokin masu gudun hijira 700 suka kama da wuta a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Karamar Hukumar Mafa, cikin Jihar Barno.

Dimbin jama’a sun rasa matsugunan su sanadiyyar tashin gobarar, wadda ta barke wajen karfe 11 na safe kuma dauki tsawon lokaci ta na cin wuta.

Ya ce wutar wadda ta samo asali daga cikin wani tanti, ta kama sauran tantinan ne saboda babu gudummawar kashe gobara da gaggawa a sansanin.

Share.

game da Author