Magu ya shafe kwanaki hudu a tsare, kullum ya na yini cur ana yi masa tambayoyi

0

Dakataccen Shugaban Rikon Hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya shafe kwanaki hudu kenan cur a tsare ana yi masa tambayoyi.

An kama Magu tun ranar Litinin, kuma tun a ranar ake tsare da shi a Ofishin Shiyyar Jami’an Bincike na CID, da ke Area 10, Abuja.

Ya na fuskantar tuhumar bincike daga Kwamitin Bincike na Musamman da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa, domin a binciki zargin da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi masa cewa ya na sace wasu kudaden da ya kwato da kuma wasu laifukan daban.

PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa a kullum Magu ya na fuskantar masu daga bangaren ‘yan sanda da SSS da kuma sauran bangarorin jami’an tsaro.

Tsohon Babban Jojin Najeriya, Ayo Salami ne Shugaban Kwamitin Bincike.

Ba Magu kadai aka gayyata domin bincike ba. Har da wasu jami’an Hukumar EFCC, amma an bar su sun tafi gidajen su bayan sun bayyana a gaban kwamiti.

Magu kadai ne ake tsare da shi.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana barin iyalan sa na zuwa ziyarar sa a inda ya ke tsare, a Ofishin CID na Area 10. Kuma a falon karbar masu ziyara ya ke kwana.

Sannan kuma lauyoyin sa na kai masa ziyara.

Kuma a kullum akan dauke shi tun karfe 9 na safe a kai shi wurin masu bincike, ana sheka masu ruwan zafin tambayoyi. Ba a maida shi Ofishin CID sai 11 na dare.

Share.

game da Author