Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce rashin dabara ce da gwamnatin tarayya ta soke zaman jarabawar da daliban shekarar karshe na sakandare za su yi ta WAEC.
Gwamnati ta soke zaman jarabawar da a baya ta ce za a yi tsakanin 5 Ga Agusta zuwa 5 Ga Satumba, ta dawo ta ce bana kwata-kwata daliban Najeriya ba za su rubuta WASSCE a 2020 ba.
Jarabawar wadda Hukumar Shirya Jarabawar Afrika ta Yamma (WAEC) ke shiryawa, tun farko gwamnatin ta dakatar da ita a watan Afrilu, wata days kafin fara jarabawar a cikin Mayu.
An dage zaman jarabawar saboda annobar Coronavirus, wadda ya zuwa yanzu sama da mutum 30,000 suka kamu a Najeriya, yayin da ta kashe sama da mutum 77.
“Matakin da gwamnati ta dauka na soke jarabawar WASSCE a 2020, dabarar-rashin dabara ce. Danyen hukunci ne, wanda a gaba zai tsame wa tsarin samar da ilmi wata kurwa a kasar nan da za ta rika addabar ilmi a kasar nan.”
Ya ce wani koma-baya ne ga matasan Najeriya milyan 1.5 da ke rubuta jarabawar WASSCE a duk shekara a Najeriya.
“Ka hana matasa masu wannan dimbin yawa rubuta jarabawa tsawon shekara daya, ka maida su baya, ta yadda na sauran kasashen duniya za su tsere musu fintikau. Ga shi kuma dan tallafin da kasashe ko hukumomi da kungiyoyin waje ke bayarwa a kan ilmi, sun dogara ne ga yadda ci gaban ilmi a kasar ke bunkasa.”
Da ya ke kawo mafita, Atiku ya ce WASSCE za ya iya shirya zaman jarabawar ta yadda yadda za a tsitstsinka daliban, ba sai an gwamutsa su a wuri daya ba, ki kuma ba sai an zauna jarabawar darasi daya a rana daya dungurugum ba.
Discussion about this post