Jihar Zamfara ta cika kwanaki 54 cur bata samu wanda ya kamu da kwayoyin Korona.
Idan ba a manta a ranar 8 ga Juni, gwamnatin Zamafara ta bayyana cewa ta shafe kwanaki 14 bata samu bullar cutar a korona ba.
Kakakin gwamnan jihar, Zailani Bappa ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ta dauka da ya sa aka samu nasarar dakile yaduwar cutar a jihar.
1 – Gwamnati Zamfara ta bi dokar gwamnatin tarayya sauda kafa tun da farkon bullowar cutar a kasar nan.
Mun rufe makarantun mu tunda wuri, mun rufe kasuwanni da iyakokin jihar mu, sannan mun saka dokar kowa ya saka takunkumin fuska dole-dole. Mun yi haka ne tun kadin cutar ta dira jihar mu ma.
2 – Kafin cutar ta bulla a Zamfara gwamtai ta kafa kwamiti biyu, daya domin wayar da kan mutane game da cutar dayan kuma domin basu tallafi
3 – Mun wadata wuraren da aka kebe domin kula da wadanda suka kamu da cutar a jihar. Mun samar da kadajen marasa lafiya akalla 100, na’aurar shakar iska, na’urar yin gwajin jutar da takunkumin fuska.
4 – kun yi wa kasuwanni feshin magani, makarantu da cikin gari baki daya.
5 – Ko a loacin da ake ta kokarin maidsa Almajirai jihohin su na asali, na mu da aka dawo da su sai da muka yi musu gwaji kafin suka shigo cikin gari.