KORONA: Malaman ‘Makarantu Masu Zaman Kansu’ na bukatar taimako da tallafi cikin gaggawa, Daga Sa’ad Azare

0

A yau wallahi tunda na tashi tunani yake ta kaini kan malaman makarantu masu Zaman kansu, wato ya kamata ace gwamnati ta taimakawa malaman nan, ganin irin halin kunci da talauci da suka fada a sanadiyyar barkewar annobar Korona, wato COVID-19 da yasa aka Kulle makarantu har yanzu.

Malaman suna bada nasu gudummawa sosai cikin Alumma musamman a bangaren Ilimi da bada tarbiyya. Sun Zabi sana’ar koyarwa dukda abinda suke iya samu baya isan su biyan bukatun su ta rayuwar yau da kullum. Kuma gudumuwar su mai girmar Gaske ne.

Yanzu a wannan lokaci na Covid-19 Allah ya kawo mu cikin wannan wani lokaci da aka kulle makarantu baki daya.

Makarantu masu Zaman kansu wato (Private Schools) ba kamar makarantun gwamnati ba ne da ko sun sun yi aiki ko basu yi ba za a caske musu albashin su, su ko makarantu masu Zaman kansu da zarar ba’a zuwa to albashin ma’aikata zai yanke ne, wato za a dakatar da shi har sai ranar da aka dawo makaranta.

Da yawa mutanen dake koyarwa a makarantu irin haka sunayi ne a rashin akin yi na gwamnati saboda babu abinda za su yi su samu na biyan bukatun su, sannan kuma da yawa daga Cikin su ma da wannan sana’a kacokan suka dogara wajen kula da kansu da iyalan su.

Don Allah gwamnati ta duba lamarin koda tsarin bada tallafin na COVID-19 ne a waiwaye malaman makarantu Masu Zaman Kan su dake fadin Kasar nan. Bayin Allah ne Kuma suna bada gudummawa wajen karfafa Ilimi amma yanzu Allah ya kawo lokacin da aka rufe makarantu kuma basu iya samun Albashi wanda da shine dama suka Dogara.

Ina wannan kiran ne tun daga mataimakin Gwamnatin tarayya zuwa jihohi da kananan hukumomi musamman yanda gwamnatin tarayya take samun tallafin Covid-19 Daga kasashen Duniya kuma take kirkiro shirye-shirye masu nagarta don rage radadin talauci da korona ta jefa Al’umma a ciki.

Comr. Sa’ad Nura Azare, 07065676868.

Share.

game da Author