JIHAR KWARA: Likitoci 12 da suka kamu da Korona sun warke

0

Shugaban kungiyar likitoci ARD dake aiki a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin UITH Lanre Olosunde ya bayyana cewa likitoci 12 da suka kamu da cutar coronavirus sun warke.

Olosunde ya sanar da haka ranar Laraba da take zantawa da manema labarai, yana mai cewa wadannan likitoci sun Kamu da cutar ne a lokacin da suke aikin duba wadanda Suka kamu da cutar a asibitin UITH.

Ya kara da cewa kungiyar ta horas da ma’aikatan lafiya kan yadda za su rika kiyaye wa da Kare Kansu daga kamuwa da cutar a lokacin da suke duba marasa lafiya.

Olosunde ya ce sun samu Karin kayan Kare ma’aikacin kiwon lafiya daga kamuwa da cutar covid-19 sannan kamfanoni masu zaman kansu a jihar sun tallafa musu da wasu kayan aikin da suke bukata.

“A yanzu ma’aikatan na da kayan aiki amma ba su Isa ba.

Bayan haka Olosunde ya ce yana sa ran cewa nan ba da dadewa ba za a sarrafa maganin kawar da cutar Coronavirus a Najeriya.

Ya ce masana kimiyya a fadin duniya na kokarin ganin an hada maganin kawar da cutar Wanda a yanzu haka an hada magunguna sama da 100 da ana can ana Yi musu gwajin inganci.

Olosunde ya Yi Kira ga mutane da su rika kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar zuwa maganin ya bayyana.

Mutum 422 suka kamu da cutar a jihar Kwara inda daga ciki mutum 229 na kwance a asibiti.

An sallami 179, mutum 12 sun mutu.

Share.

game da Author