Wasu kwararrun likitoci daga kasar UK sun shaida cewa sinadarin ‘Vitamin D’ baya warkar da cutar coronavirus.
Likitoci sun fadi haka ne ganin yadda wasu mutane ke fadin cewa sinadarin ‘Vitamin D’ na da ingancin warkar da cutar coronavirus.
Sinadarin ‘Vitamin D’ na kara karfin kashi, inganta karfin garkuwan jiki sannan yana kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake sa a samu matsalar toshewar numfashi, kuma wara na da wannan sanadari.
A dalilin haka likitoci ke Kira ga mutane da su rika cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Vitamin D’ domin inganta garkuwar jikinsu amma ba domin su kare kansu daga kamuwa da cutar coronavirus ba.
Abincin dake dauke da sinadarin Vitamin D sun hada da:
1. Dafaffen kwai
2. Lemun Zaki
3. Hanta dafaffe ko Kuma soyayye
4. Kifi
5. Madara
6. Madaran waken soya
7. Wara
8. Kubewa