Yadda Jami’an tsaro suka damke Magu, suka yi awon gaba da shi zuwa fadar shugaban kasa da karfin tsiya

0

Jami’an tsaro sun yi wa Karamin Ofishin EFCC da ke Wuse II kawanya, su ka damke Shugaban EFCC din na Riko, Ibrahim Magu.

An yi awon gaba da shi da rana, bayan jami’an tsaron sun kwashe minti 30 su na tankiya da jami’an tsaron Magu.

Sun dai hana masu tsaron Magu bin su, domin su ga inda aka nufa da shi.

An garzaya da shi cikin Fadar Shugaban Kasa, domin amsa tambayoyi daga kwamitin binciken da Shugaban Kasa ya kafa, domin binciken zargin da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi masa.

Malami dai ya zargi Magu da yi wa shirin yaki da rashawa kafar-ungulu da kuma yi wa wasu kudaden da Hukumar EFCC ta kwato, irin abin nan da Hausawa ke kira ‘sata-ta-saci,-sata.’

Majiya daga EFCC ta ce tuni har lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya garzaya Fadar Shugaban Kasa inda Magu ya ke a yanzu.

Ko EFCC ko SSS babu wanda ya ce komai dangane da kamun da aka yi wa Magu.

Jami’an Yada Labaran su ma da aka kira, kin cewa komai suka yi.

Share.

game da Author