Tantirin dan damfarar nan Ramon Abbas (Hushpuppi), dan Najeriya da ya buwayi duniya, amma a karshe ya fada hannun jami’an FBI na Amurka, ya ce labarin rayuwar sa zai karfafa guyawun ‘yan Najeriya su sa ran yin gam-da-katarin ‘kyakkyawar madogara’.
Hushpuppi ya ce labarin sa zai sosa rayuka da zukatan ‘yan Najeriya masu yin rayuwar dindindin a cikin kuncin talauci, fatara da yunwa.
Ya yi wannan bayani cikin wasu fayafayen bidiyon da suka bayyana a soshiyal midiya bayan an damke shi a Dubai.
Yanzu haka Hushpuppi na hannun FBI a Amurka, inda zai fuskanci tuhuma kan damfarar da ya rika yi wa dimbin jama’a ta intanet a Amurka da sauran kasashen duniya ta milyoyin daloli.
Hushpuppi ya yi kaurin suna a Dubai inda ya ke da zama, ta yadda yadda ya rika dakasharama, tabargaza da ragargazar kudade.
Ya rika tafiyar da rayuwar sa wajen sayen komai Mai tsadar gaske a duniya, tare da rika bayyana dukiyoyin da ya mallaka a soshiyal midiya.
“…ku da ke ta surutan banza a kai na, kamata ya yi ku yi amfani da labari na domin ku ba marasa galuhu kwarin-guiwar samun kyakkyawar madogara.” Inji Hushpuppi cikin wani bidiyo.
“Amma sai surutai ku ke ta yi ku na jin cewa al’umma ba za su yi gam-da-katar a rayuwa ba. Ku a tunanin ku kawai zama cikin kuncin rayuwar talauci ce ta dace da ni.”
Duk wadannan bayanai a cikin ‘broken English’ ya rika yin su.
Ya ce dimbin ‘yan Najeriya na rayuwar hannu-baka-hannu-kwarya saboda rashin gwamnatin kwarai a Najeriya.
Ya ce mahaifiyar sa ‘yar asalin yankin Neja Delta ce, yankin da arzikin man fetur din da Najeriya ke tutiya da shi. Amma ba ta taba cin moriyar ko sisi na wannan dimbin arziki da ke a yankin na su ba.
“Mutanen Neja Delta ma ba su ci moriyar dukiyar yankin su ba, balle a yi maganar wadanda ke Badagry da Agege. Ko ci gaba ya je muku ne?
“Ina mutanen Ebonyi? Me aka tsinana muku. Sau da yawa ina kallon labarai. An dauke su kamar ba ‘yan Najeriya ba. Saboda ci gaba bai kai wurin su ba. Shin ba su cancanci jin dadin rayuwa ba ne?”
Abbas ya rika yin bidiyon a matsayin raddi ga ‘yan Najeriya wadanda ke caccakar sa.
An nuni shi yadda yadda ya yi shatar jirgi daga Dubai zuwa Faransa, har shigar sa kasaitaccen otal din kasar.
An kuma nuno abokan sa na bayanin yadda direban sa ke karbar albashin naira 700,000 a wata. Shi kuma mai yi masa wanki naira 259,000 a wata.
Hushpuppi ya damfari mutane da yawa a duniya, ciki har da wata kungiyar kwallon kafa na Premier da ke Ingila, wadda ya damfara dala milyan 124.
Hushpuppi dai ya ce shi ba dan damfara ba ne, manajan shirya bukukuwa ne. Aikin sa shi ne shirya wa kasaitattun mutane buki su na biyan sa.