Kungiyar Likitocin na ARD dake aiki a asibitin koyarwa na Olabisi Onabanjo dake jihar Ogun sun fara yajin aiki.
Kungiyar ta ce ta fara yajin aikin ne saboda rashin biyan bukatun su da Gwamnati ta ki yi.
Wadannan bukatu na kungiyar sun hada da rashin saka likitoci cikin tsarin inshoran lafiya, rashin biyan ma’aikata da sabon tsarin biyan albashin ma’aikata, rashin biyan su alawus, rashin Kara wa ma’aikata girma da sauran su.
Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Yuli Kungiyar ARD ta fara yajin aiki amma banda Likitocin dake kula da masu fama da cutar covid-19 a jihar.
Sai dai a ranar Laraba kungiyar ta umurci Likitocin dake kula da wadanda Suka kamu da cutar covid-19 da su fara yajin aikin.
A ranar 13 ga watan Yuli Kungiyar likitocin jihar Legas karkashin ‘Medical Guild’ ta yi barazanar daina zuwa aiki a duk asibitocin da ake kula da masu fama da cutar coronavirus a jihar na tsawon kwanaki uku har Sai gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Bukatun kungiyar sun hada da rashin biyan Likitoci albashin su na tsawon watanni biyu, banbanta albashin Likitocin dake aiki da gwamnati jihar da na gwamnati tarayya, rashin biyan su alawus, rashin Samar da isassun kayan Samun kariya daga Korona, rashin inshorar lafiya wa ma’aikata da rashin isassun likitoci a asibitocin gwamnati a jihar.
A dalilin wadannan matsaloli kungiyar ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 21 domin ta biya bukatunsu inda a ranar 27 ga watan Yuni wadannan kwanaki suka cika, kuma ta kara wa gwamnati kwanaki 14.
Kungiyar za ta zauna bayan wa’adin kwanaki ukun da ta bada sun cika domin tattauna matakin da za su dauka a gaba.