Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 643 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –230, Oyo 69, FCT 51, Edo 43, Osun 35, Rivers 30, Ebonyi 30, Kaduna 28, Ogun 27, Ondo 23, Filato 20, Benue 17, Enugu 16, Imo 10, Delta 6, Kano 4, Nasarawa 2, Kebbi 1, Ekiti 1
Yanzu mutum 34,259 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 13,999 sun warke, 760 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 19,500 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 12,941, FCT – 2,738, Oyo – 1,951, Edo – 1,850, Delta – 1,398, Rivers – 1,427, Kano – 1,318, Ogun – 1,132, Kaduna – 1,067, Katsina – 1,726, Ondo – 770, Borno – 593, Gombe – 533, Bauchi – 521, Ebonyi – 646, Filato – 591, Enugu – 531, Abia – 413, Imo – 409, Jigawa – 321, Kwara – 422, Bayelsa – 318, Nasarawa – 254, Osun – 311, Sokoto – 153, Niger – 145, Akwa Ibom – 145, Benue – 143, Adamawa – 110, Anambra – 101, Kebbi – 88, Zamfara – 76, Yobe – 62, Ekiti – 67, Taraba- 30, Kogi – 5, da Cross Rivers – 10.
Hukumar UNODC dake karkashin majalisar dinkin duniya ta gargadi mutanen kasashen duniya da gwamnatoci, su rika sara suna duban bakin gatari da kuma jan kunnen mutane game da nisanta daga yin mua’mula da tsuntsaye da namun daji.
Rahotan ya nuna cewa Kashi 75 bisa 100 na cututtukan da ake fama da su a duniya na da alaka da cin namun daji.
Rahoton ya kuma nuna cewa cutar SARS-CoV-2 Wanda ya haifar da cutar coronavirus na da alaka da wata dabban daji mai suna pangolins
Shugaban UNODC Ghada Waly, kwamishinan EU Jutta Urpilainen da shugaban ‘Convention on International Trade in Endangered Species of Wild Fauna and Flora (CITES)’ Ivonne Higuero sun yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukan matakan da za su taimaka wajen hana farautar namun daji domin kare muhalli, dabbobin daji da kiwon lafiyar mutane a duniya