“Ban sani ba ko nan gaba zan fara siyasa, amma a yanzu A’a” – Rahama Sadau

0

Jarumar fina-finan Najeriya da ta yi fice a farfajiyar Shiya fina-finan Hausa, wato Kannywood da da kuma fina-finan Legas, Rahama Sadau ta bayyana cewa akwai maza da dama da suke nuna suna sonta da aure amma a duk lokacin da suke bayyana ra’ayin su, sai ta ce musu,  ta gode.

” yawanci sai dai na yi dariya ko kuma na ce na gode,”  haka kuma jarumar ta ce bata da saurayi ko daya a farfajiyar Kannywood.

Rahama ta furta wadannan kalamai ne a hirar ta BBC Hausa a makon jiya.

Bayan haka ta bayyana yadda zaman Gida Dole saboda Korona  da aka sa kowa yayi a Najeriya ya takurata matuka.

“Lokacin kullen sai dai mutum ya yi ta yin kame-make. Ka yi karatu ya ishe ka, ka yi kallo ya ishe ka, ka yi chatting ya ishe ka, na ji kamar zan mutu.

Ta kara da cewa wannan zaman gida na dole da aka yi ne ya sa sam-sam ba a ji duriyarta ba a kafafen sada zumunta kamar a baya ba.

Rahama ta kara da bayyana yadda wannan zaman gida na dole ya kawo wa sana’ar su cikas.

” Sana’armu na bukatar a rika tara jama’a kuma yanzu an hana yin hakan saboda wannan annoba saboda haka a mu dai Korana ta fi shafar su fiye da kowa a ganina.

A karshe jarumar ta yi bayanin yadda ta kammala karatun digirinta a kasar Cyprus, da yun kira ga masu fada aji a kasa su gaggauta daukar matsaya da matakin game da kawo karshe yawaita yin fyade da ake yi wa mata kanana a kasar nan.

“Nakan tambayi mutane wannan abin da ke faruwa da gaske ne… wasu za ka ga ‘ya’yansu suke wa. Wai duk na mene ne,”

Game da siyasa kuma jarumar ta ce,

” Ban sani ba ko a nan gaba zan fara siyasa, amma a yanzu a’a,”

Share.

game da Author