Kungiyar Makarantu masu Zaman kansu da na Iyayen Dalibai sun nuna rashin amincewar su ga hukuncin da ministan Ilmi Adamu Adamu ya yanke na dakatar da yin jarabawar WAEC a Najeriya.
Shugaban Kungiyar Makarantu masu Zaman kansu ta Kasa, NAPPS, Yomi Otubela ya bayyana cewa lallai wannan gurguwar shawara ce ministan Adamu ya dauka domin kuwa su Makarantu masu Zaman kansu a shirye suke domin tabbatar da an bi dokar hukumar NCDC a lokacin da za a rubuta jarabawar.
” Dukka Makarantu masu Zaman kansu a sun shirya tsaf, za su samar da yanayin da ya dace a lokacin da dalibai suka fara zana jarabawar. Muna rokon ministan ya canja wannan matsayar tasa ya bari a rubuta jarabawar kamar yadda WAEC ta shirya kuma ta tsara.
Shima shugaban kungiyar Iyayen dalibai na Najeriya,Haruna Danjuma ya soki wannan matsayar na gwamnati.
” Akwai rudani cikin wannan hukunci da ministan ya yanke game da zana jarabawar WAEC din. Idan ba a manta ba kwamitin shugaban Kasa ta ce za a iya bude makarantu domin daliban ajin karshe su rubuta jarabawar WAEC din. Amma kuma kwatsam sai gashi ministan Ilmi ya fito ya some wannan umarni na kwamitin shugaban Kasa.
” Abinda ya kamata su gwamnati ta sani shine idan banda Turanci, Lissafi da Biology, babu wani jarabawa da zai Tara dalibai da yawa a wuri daya. Wasu ma darussan kamar Geography, Government da sauransu ba za a samu dalibai fiye da 40 ba.
” Kuma ma dai idan har za a yarda a bude kasuwanni, Masallatai, Otel ad wasu wuraren da ke tara jama’a me zai hana a bari yara su rubuta jarabawar karshe ba. Sannan kuma a haka aka rubuta jarabawar JAMB, duk ba a samu matsala ba sai WAEC.
Ita ko hukumar WAEC ta bayyana cewa tana aiki me a kasashe biyar dake yankin Afrika ta Yamma, kuma tare da hadin guiwar gwamnatocin wadannan kasashe.
” Ba za mu iya yin gaban Kan mu ba game da wannan matsala, dole sai mun shawarci kasashen da muke aiki a ciki da kuma matsayar gwamnatocin su kafin mu iya daukar matsayar a Kan abinda muka da a gaba.
Discussion about this post