Tsohon mai ba shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki ya karyata rahotannin wasu jaridun kasar nan da suka ruwaito cewa wai yayi wa APC aiki a 2015.
” Babu abinda ya hada ni da APC a zaben 2015, kuma ni ban yi wa Buhari yakin cin zabe a bayyane ko a boye ba.” Inji Dasuki.
Dasuki ya bayyana cewa abinda ya sani ya auku shine, a lokacin da ake kokarin yin maja tsakanin jam’iyyar ACN da CPC, da shi a cikin wadanda sukayi ta kai komo majar ya tabbata a 2011, amma kuma da hakan bai yiwu ba sai ya tsame hannun sa kwata-kwata.
” Da dai ban so in ce komai ba game da wannan labari da ake ta yadawa, sai kuma na ga cewa ya kamata in fadi wa duniya gaskiyar abinda ke a kwai maimakon in bari ayi ta yada karerayi.
” Ko a lokacin da Jonathan ya nemi in zama masa maiba da shawara kan harkakin tsaro, na gaya masa cewa ina da kyakkyawar alaka da Shugaban CPC a wancan lokaci, Muhammadu Buhari, Bola Tinubu na ACN da da Ogbonnaya Onu na ANPP. Kuma na gaya masa cewa ba zan butulce shi ba koda ya bani damar yi aiki da shi.
” Kuma ina tabbatar muku a yau cewa ban taba ko da da wasa ba, yi wa Jonathan yankan baya ba ta hanyar garzaya wa a boye in ci amanar da ya bani ba don alaka ta ta Buhari, Tinubu da Ogbonnaya Onu. Na yi aiki na tsakani da Allah, kuma shi ma Jonathan ya san haka.
” Saboda haka wannan labari, karya ce, babu abinda ya hada ni da Buhari, ko jam’iyyar APC tun daga 2012 zuwa zuwa 2015.
Discussion about this post