Amurka ta koro ‘yan Najeriya sama da 3,000 da suka aikata muggan laifuka

0

A kokarin da kasar ke yi domin rage tururuwar masu hijira su na tarewa a can, Amurka ta koro ‘yan Najeriya har 3019 a cikin shekaru 15.

Wani bayanin da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Amurka ta bayyana kwanan nan, ya nuna cewa wadanda aka taso keyar ta su zuwa gida duk su na da bakin tambarin aikata muggan laifuka a lokacin in da suke zaune Amurka.

Daga cikin mutum 5,892 da Amurka ta maido Najeriya, daga 2003 zuwa 2018, 3,019 cikin duk sun taba aikata muggan laifuka.

Wannan adadin ‘yan Najeriya da aka maido, shi ne ya fi na sauran kasashen Afrika muni, yayin da Amurka ta maido ‘yan Amurka 20, 178 a cikin shekara 15.

Akasarin ‘yan Najeriya da Afrika baki daya da aka maido, masu muggan laifuka ne, sai wadanda suka shiga ba bisa ka’ida ba, da kuma mazambata da ‘yan harkalla.

Dama a cikin 2016 Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin korar Afrikawa “kusan milyan 2” da ya ce masu aikata muggan laifuka ne, ‘yan kwaya da mazambata. Ya ce za mu zakulo su mu kora su zuwa kasar su.

A tsawon wadannan shekaru, yawancin ‘yan Najeriya da aka taba daurewa Amurka, sun aika fashi da makami ne, 419, fyade, fojare, sane da kisa.

Share.

game da Author