Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 790 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -120, Delta 166, Enugu 66, FCT 65, Edo 60, Ogun 43, Kano 41, Kaduna 39, Ondo 33, Rivers 32, Bayelsa 29, Katsina 21, Imo 20, Kwara 18, Oyo 11, Abia 10, Benue 6, Gombe 4, Yobe 2, Bauchi 2 da Kebbi 2.
Yanzu mutum 26,484 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 10,152 sun warke, 603 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 10,630, daga nan sai FCT – 1,935, Oyo – 1,391, Kano – 1,257, Rivers – 1, 088, Edo – 1,165, Delta –1,131, Ogun –869, Kaduna – 805, Katsina – 578, Bauchi – 505, Gombe – 507 125 363 19, Borno – 493, Ebonyi – 438, Filato – 382, Jigawa – 318, Imo – 352, Abia – 320, Enugu – 327, Ondo – 325, Kwara – 235, Nasarawa – 213, Bayelsa – 234, Sokoto – 151, Osun – 127, Akwa Ibom – 86, Adamawa – 84, Niger – 116, Kebbi – 81, Zamfara – 76, Anambra – 73, Yobe – 61, Benue – 65, Ekiti – 43, Taraba- 19 da Kogi – 4.
Idan ba a manta ba, a ranar Talata, Hukumar Lafiya ta duniya (WHO), ta bayyana cewa yanzu ne duniya za ta afka cikin babban bala’in Coronavirus.
Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya fitar ya ce a baya ba a ga komai ba tukunna.
Tedros wanda aka buga bayanin sa a BBC da rumbun tattara bayanan kamuwa da kisan adadin mutane sakamakon Coronavirus, wato worldometers.org suka wallafa, ya ce matsawar gwamnatocin kasashen duniya ba su gaggauta tashi tsaye sun yi da gaske ba, to wannan cuta za ta yi wa duniya rundugun da ya wuce wanda ake ciki a yanzu fiye da kima.
Discussion about this post