Majalisa ta nemi a dakatar da Shirin Daukar 774, 000

0

Majalisar Dattawa da ta Tarayya, sun nemi a dakatar da Shirin Gwamnatin Tarayya na daukar kananan ma’aikata 774, 000, har sai an yi mata bayani gamsasshe dangane da yadda ake bi ana daukar ma’aikatan.

Hakan ya biyo bayan tankiyar da ta faru ce tsakanin Karamin Ministan Kwadago, Fesrus Keyamo da kuma Kwamitin Lura da Ayyuka da Ma’aikata na Majalisar Dattawa a ranar Talata.

Cikin wata sanarwar hadin-kai da Majalisar Dattawa da ta Tarayya suka fitar a ranar Laraba, sun amince cewa a tsaida shirin, jar sai Babban Ministan Kwadago, Chris Ngige da dukkan masu ruwa da tsaki a batun shirin daukar leburorin sun bayyana a gaban kwamiti sun yi gamsasshen bayanin matakan da suke bi wajen daukar ma’aikatan.

Daukar ma’aikatan ta zo da rikici, saboda an raba wa manyan kasar nan adadin da kowane bangare zai kawo sunayen su.

Yayin da Majalisar Dattawa ke zargin Keyamo da cuwa-cuwar sunaye, shi kuma ya yi musu bambami ne saboda ya yi zargin cewa su na neman kwace shirin daga hannun su, duk kuwa da cewa an ba su guraben kawo sunayen leburori har kashi 10% na adadin da za a dauka aikin.

PREMIUM TIMES ta buga labarin bobbotan da Karamin Minista Keyamo ya yi a gaban Kwamitin Majalisa, wanda sanadiyyar hakan har Sanata Ifeanyi Uba ya maida masa raddin cewa Minista Keyamo dan jagaliya ne, shi ya sa ya yi bambami a Majalisa -Sanata Ubah

Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, ya bayyana bobbotan da Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo ya yi a Majalisar Dattawa da cewa dabi’a ce ta dan jagaliya da ‘yan tasha.

Ya ce ya na mamakin yadda Keyamo ya rika hauragiyar tunanin cewa Sanatoci na kokarin kwace daukar leburorin aiki daga hannun sa.

Ya yi wannan raddi ne a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, ranar Laraba, inda ya yi matashiya cewa aikin Sanatoci shi ne sa-ido kan ayyukan da Ministoci ke yi, kuma shi Keyamo din ya san haka.

PREMIUM TIMES ta buga lanarin yadda Keyamo ya rika hayagaga da bambami a zaman sa Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa a ranar Talata.

An shirya taron ne domin su san inda aka kwana game da batun daukar ma’aikatan leburodi 774,000 da gwamnatin tarayya ta ce za ta dauka aiki.

A cikin Kasafin 2020, Majalisar Dattawa ta amince da kashe naira bilyan 52 wajen biyan wadannan leburori da kuma ayyukan da za su rika yi a fadin kasar nan.

Za a dauki lebura 1,000 a kowace Karamar Hukuma a fadin kasar nan cikin Kananan Hukumomi 774.

Keyamo ya zargi Sanatoci da kokarin yin banakeren kwace yawan leburorin da za a dauka, duk kuwa da cewa an ba su alfarmar kawo leburori a dauka aikin har adadin kashi 15% daga cikin 774, 000 da za a dauka aikin.

Sanata Ubah ya ce Sanatoci ba su yi laifi ba don sun tambayi yadda aka raba daukar ma’aikatan.

A matsayi na na sanatan da ke wakiltar jama’a, hakki na ne na binciki yadda ya ke tafiyar da tsarin daukar leburin a kasar nan. Saboda abin ya shafi wadanda na ke wakilta. Sannan kuma wanda aka damka wa aikin daukar leburorin na cikakken Minista ba ne, na je-ka-na-yi-ka ne.

“Ni ban san abin da Minista ke nufi ba, da ya yi kane-kane wajen daukar leburorin da za a rika biya ladar naira 20,000 ko 30,000 a wata ba. In banda dan tasha da dan jagaliya, ya daga mun yi maka tambaya za ka kama cika ka na batsewa, ka na ihu da kwaratsatsa?

“Mu ne ya kamata a bai wa damar dauka ko kawo sunayen wadanda za a dauka.

“Amma damka aikin a hannun dan jagaliya da zai je ya yi harkallar raba guraben ayyukan, abu ne da ba za mu amince ba.”

Asalin Yadda Batun Daukar Leburori 774, 000 Ya Taso:

Matasa 774,000 da za a dauka aiki, za su yi kwalbati, shara da hanyoyin burji a biya su naira 20,000 a wata -Minista Keyamo

Karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo, ya bayyana dalla-dallar irin ayyukan da matasa 774,000 da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar cewa tuni an fara shirin daukar su aiki a dukkan kananan hukumomin kasar nan.

Da ya ke ganawa da manema labarai kwanan baya, Keyamo cewa ya yi sai ranar 1 Ga Oktoba matasan za su fara aiki.

Sannan kuma ya ce a ranar, za a fara ne da gwaji a jihohi takwas tukunna.

Jihohin da Kiyamo ya ce za a fara aikin sun hada da Adamawa, Barno, Ekiti, Ebonyi, Edo, Jigawa, Kwara da kuma Katsina.

Minista Keyamo ya ce za a fara ne da matasa 40,000 a wadannan jihohi takwas, kafin daga nan kuma a ci gaba a sauran jihohin kasar nan.

Irin Ayyukan Da Za Su Rika Yi A Kan Naira 20,000 A Wata:

Keyamo ya ce ayyuakan na su akasari duk ci-da-karfin-ka ne da suka hada da:

1. Yin amfani da diga da cebur da minjagara su na ginin kwalbatoci, ginar ramu da kuma aikin fitikin sare ciyawar da ke gefen titi.

2. Sassabe, shara da kaftun hanyar ruwan da ke kwarara daga madatsar-ruwa zuwa cikin cikin gonakin noman rani.

3. Aikin ginin hanyoyin shararra da burji da gyaran hanyoyin.

4. Rainon sabbin shuke-shuken itatuwa da yi musu ban-ruwa a jihohin Jigawa, Barno da Katsina.

5. Kula da warware matsalar cinkoson ababen hawa a kan titina.

6. Shara da goge-goge a makarantu, asibitoci da wasu ofissoshin gwamnati.

Premium Times Hausa ta buga labarin albishir din da Buhari ya yi a Ranar Dimokradiyya cewa gwamnatin sa ta fara Shirin Samar Da Ayyukan Musamman ga
matasa 774,000, don yaye musu talaucin Coronavirus.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Gwamnatin sa ta fara wani gagarimin shiri na gaggauwar daukar matasa 774,000 aiki na musamman, domin yaye musu kuncin rayuwar da jama’a suka shiga sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus.

Da ya ke jawabi a ranar Juma’a yayin tunawa da Ranar Dimokradiyya, wadda ta koma 12 Ga Yuni, Buhari ya ce cutar Coronavirus ba karamar illa ta yi wa milyoyin jama’a ba.

“Da yawa sun rasa iyalai, ‘yan uwa da masoyan su. Wasu sun rasa aikin su baki daya. Milyoyi sun rasa dukiyoyin su. Tattalin arzikin wasu ya karye dalilin cutar Coronavirus.”

A kan haka ne Buhari ya ce gwannatin sa ta raba kayan tallafin rage radadin talauci da kuma raba bilyoyin kudade ga milyoyin marasa galihu a kasar nan.

Da ya juya a kan ayyukan musamman da ya ce gwamnatin sa za ta samar wa matasa kwanan nan, Buhari ya ce za a tsamo matasa 1,000 ne daga kowace karamar hukuma daga Kananan Hukumomi 774 da ake da su a fadin kasar nan.

Ya bada hakuri dangane da irin matsanancin halin kuncin da ‘yan Najeriya suka shiga, dalilin tsauraran matakan da gwamnatin tarayya ta dauka domin kokarin dakile cutar Coronavirus.

Ya ce cutar abin tsoro ce ganin yadda ta fara kamar da wasa a kasar China, amma ga shi cikin ‘yan watanni ta shafi mugum sama da milyan 7 a duniya a cikin kasashe 216.

Ya ce jo shakka babu Coronavirus babbar barazana ce ga rayuwar dan Adam gaba daya a duniya da kuma tattalin arzikin duniyar baki daya.

Idan ba a manta ba, Buhari ya rasa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari sanadiyyar cutar Coronavirus da ya dauko a kasar Jamus.

Kyari dai an yi ittifakin cewa a gwamnatance, shi ne mutumin da ya fi kowa kusanci da Buhari, kafin Coronavirus ta yi sanadiyyar ajalin sa.

Share.

game da Author