Masu garkuwa da mutane sun sace alkalin kotu mai suna Donatus Shidda a jihar Taraba.
Wani makwabcin Shidda wanda ba ya so a fadi sunnan sa ya ce maharan sun dira gidan Shidda dake garin Jalingo da misalin karfe 5 na safiya.
” ‘Yan bindiga sun far wa gidan ne suna rike da bindigogi daga nan suka dauke shi suka yi awon gaba da shi.
” Ko da na isa gidan bayan maharan sun arce, sai na iske matar alkalin Shidda tsugune tana ta sharba kuka.
“Har yanzu dai maharan ba su kira iyalan Shidda ba amma mun sanar wa ‘yan sanda abin da ya faru.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandar jihar David Misal ya tabbatar da haka sannan ya ce jami’an tsaro sun fantsama farautar wadannan masu garkuwa da mutane a jihar.