Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da fara tilasta wa jihohin tarayyar kasar nan fara aiki da Dokar Musamman Ta 10, wadda ta bai wa Majalisun Jihohi da Bangaren Shari’a na Jihohi ikon cin gashin kan su gada hannun gwamnatin jihar su.
Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya sanar wa manema labarai haka a ranar Litinin a Abuja, bayan wasu gwamnoni sun gana da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Ministan Shari’a da kuma Ministar Harkokin Kudade.
Fayemi ya ce sun je Fadar Gwamnatin Tarayya domin yin bayanin yadda Buhari zai fahimci cewa Dokar Musamman ta Shugaban Kasa mai lamba 10 da ya rattaba wa hannu, akwai wasu wuraren da ta ci karo da dokar kasa.
Ya ce a kan haka Buhari ya dakatar ko kuma zai yi jinkirin tilasta fara aiki da ita tukunna har sai an warware wuraren da kulli ya cukurkude.
Fayemi ya kara da cewa an kafa kwamiti a karoashin Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal da wasu gwamnoni, inda suke ganawa da Shugabannin Majalisar Jihohi domin fahimtar yadda mishkilar ta ke.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu kan Dokar Cin-gashin-kan Majalisar Dokokin Jiha da Bangaren Shari’a na jiha.
A ranar Juma’a ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan Dokar Musamman ta Cin-gashin-kan Majalisar Dokokin Jihohi da bangaren shari’un fadin kasar nan.
A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya bai wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya umarnin cire wa Majalisar Dokoki ko Bangaren Shari’a kudaden su daga asusun duk wata jihar da ta ki bin wannan umarni.
Wannan doka dai ta na nufin kudaden da gwamnatin tarayya ke bai wa Majalisar Jihohi da bangaren shari’a na jihohi 36 da Abuja, ba su kara makalewa asusun jiha, ana jekala-jekalar sai yadda gwamna ya ga damar bada kudaden.
Kakakin Yada Labarai na Ministan Shari’a, Abubakar Malami, mai suna Umar Gwamdu ne ya fitar da wannan sanarwa, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES, a madadin ministan.
Wannan doka mai suna Doka Ta Musamman Ta 10, Ta 2020, ta bai wa gwamnoni umarnin shigar sa Majalisar Dokokin da bangaren shari’a cikin kasadin kudi, tun tashin farko.
Tuni har an bada umarnin kafa kakkarfan kwamitin da zai aikin shimfida ka’idoji, sharudda, hakki da kan-iyakokin da kowane bangare ke da ikon cin-gashin-kai, kamar yadda dokar Sashe na 121 (3) na Dokar Najeriya ta 1999 ya tanadar.
Wannan doka ta haramta wa gwamnonin jihohi rike wa Majalisar Dokokin Jiha da bangaren shari’ar jihar dukkan hakkokin su.
Kuma dokar ta umarci duk gwamnan da ya ki bin dokar, to a Akanta Janar na Tarayya ya cire kudaden majalisa da na kotuna da alkalan daga kason kudaden da gwamnatin tarayya ke tura wa jihar a duk wata.