Dan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar, Adamu Atiku kuma kwamishinan ayyuka na jihar Adamawa, ya bayyana cewa mahaifin sa Atiku Abubakar zai sake fitowa takarar shugabancin Najeriya.
Atiku ya fadi haka da yake zayyano nasarorin da ma’aikatar sa ta samu a tsawon shekara daya na mulkin gwamna Ahmadu Fintiri a jihar Adamawa.
” Babu abinda zai hana mahaifina, Atiku Abubakar fitowa takara kujerar shugabancin Najeriya a 2023, zai yi takara domin fitaccen dan siyasa ne kuma jajircacce ga kuma kwarewa.
Bayan haka Adamu ya ce akwai yiwuwar shima kan sa yayi takarar kujerar Sanatan shiyyar sa a 2023.
Idan ba a manta ba say biyar Atiku na tsayawa takarar shugabancin Najeriya, amma baiyi nasara ba tun daga 1993 zuwa 2019.
Wanda ke biye masa shine Muhammadu Buhari da yayi takara sau hudu.