Yadda cutar Korona ke rage karfin aikin da maganin ‘Antibiotics’ ke yi a jikin mutum – WHO

0

Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta nuna fargaban cewa rashin aikin maganin ‘Antibiotics’ a jikin mutum zai karu saboda yadda ake amfani da maganin wajen kau da cutar Covid-19 a duniya.

Antibiotics magani ne dake warkar da cutar dake da dauke da kwayan cuta da ake kira ‘Bacteria’ sannan yana daya daga cikin magungunan da likitoci ke baiwa mai dauke da cutar Covid-19 a asibiti domin ya warke.

WHO ta ce yawaita amfani da maganin wajen warkar da masu fama da cutar Covid-19 na iya hana maganin aiki a jikin mutum nan gaba.

WHO ta ce kasashe 150 sun ce maganin ba ya yi wa mutanen kasashen su da suka kamu da cutar magani a jiki ba.

Sun ce hakan na da nasaba ne da yadda ake amfani da maganin ta hanyoyin da bai kamata ba musamman ba tare da umarnin likitoci ba.

WHO ta ce bincike ya nuna cewa wanda cutar bata yi tsanani a jikin da ba ko kuma wanda ake zaton ya kamu da cutar basu bukatan maganin ‘Antibiotics’.

Jami’ar WHO Hanan Balkhy ta ce ware kudade domin gudanar da bincike da gano hanyoyin da suka fi dacewa wajen kula da masu fama da cutar Covid-19 da sauran cututtuka da ake amfani da maganin ‘Antibiotics’ domin warkar da su na cikin hanyoyi da za su taimaka wajen hana rashin aikin maganin a jikin mutane.

WHO ta tsara wasu hanyoyi da Za su taimaka wajen magance cututtukan dake ake amfani da maganin domin warkar da su.

Share.

game da Author