KORONA: Masari ya janye dokar Zaman Gida Dole a Katsina

0

Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Aminu Masari, ta janye dokar zaman gida dole da ta saka a jihar saboda kokarin dakile yaduwar cutar Covid-19.

A sanarwar Wanda sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa ya rabawa manema labarai a Katsina, gwamnati da saka dokar Hana walwala daga karfe 10 na dare zuwa 4 na Asuba.

“A dalilin samun raguwar yaduwar cutar da aka samu a jihar da Kira da mutane suka yi na a rika bari ana gudanar da harkoki irin na cinikayya da saboda rugujewar tattalain arzikin da jihar ke fama da shi a dalilin garkame gari ya sa gwamnati ta bude gari.

Gwamnati ta yi kira ga mutane da su kiyaye dokokin kaucewa kamuwa da cutar Korona kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta jiha ta zayyano tare da kiyaye sharuddan samar da tsaro da Jami’an tsaro suka bada.

Inuwa ya ce dokar hana tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin na nan daram sannan da dokar Hana acaba da Keke Napep daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe shima na nan.

Ya ce idan mutane ba su kiyaye sun bi dokokin da gwamnati ta saka ba lallai zai sa gwamnati garkame jihar gaba daya.

Inuwa ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokarin wajen ganin ta dskile yaduwar korona a jihar.

Gwamnati ta garkame kananan hukumomin Batagarawa da Daura a dalilin yawan wadanda suka kamu da ake samu daga wadannan kananan hukumomi.

Share.

game da Author