Yadda aka yi wa Babban Jojin Katsina rufa-rufa ya saki ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da Ahmed Sulaiman

0

Babban Jojin Jihar Katsina, Musa Abubakar ya shiga cikin tsomomuwa, bayan wasu ‘yan ragabzar ma’aikatan sa sun masa rufa-rufa, ya bada belin ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da fitaccen mai jan baki na Kungiyar Izala, Ustaz Ahmed Sulaiman.

An yi garkuwa da malamin ne cikin watan Maris, 2019 a tsakanin Sheme da Kankara, lokacin da ya ke kan hanyar komawa Kano daga Kebbi.

Daga baya jami’an tsaro sun kama wadanda ake zargi, kuma da kan su suka yi ikirarin cewa su na da hannu a tsare shi tare da sauran abokan tafiyar sa.

A yanzu kuwa hayaki ya tirnike a bangaren shari’a a Katsina, bayan da Cif Joji Musa Abubakar ya sa hannun bada belin rikakkun masu garkuwa da mutanen, ba tare da kotu ta bayar da belin su ba.

Babban Rajistara na Babbar Kotun Katsina, Kabiru Sha’aibu, ya ce wasu dibgaggun ma’aikatan shari’a ne suka tsara takardun beli na gidoga, suka kai wa Cif Joji ya sa hannu, tun kafin Mai Shari’a na Babbar Kotun Katsina ya zauna zaman sauraren yiwuwar beli ko a’a.

Wani lauya dan Kungiyar Lauyoyin Jihar Katsina mai suna Yusuf Dauran, ya yi karin haske kan wannan dambarwa, bayan damke shi da jami’an tsaro suka yi, bisa zargin sa da hannu, a matsayin sa na lauyan wadanda ake tuhuma din.

Da ya ke wanke kan sa daga zargin, Dauran ya ce shi kan sa ya yi mamakin ganin yadda Cif Joji sukutum ya sa hannun bada belin ‘yan bindigar, alhali alkali bai ma zauna ya yanke hukuncin bada belin su ba.

Ya ce shi ya je Babbar Kotu ya shigar da takardar neman beli. Don haka ranar zaman kotu kawai ya ke saurare. Amma abin daure kai, sai ya ji wai Cif Joji ya sake su.

Shi ma Mataimakin Sakataren Kungiyar Lauyoyin Katsina, Ibrahim Babangida, ya ce su na kira ga jami’an SSS da suka gaggauta sakin lauya Dauran, domin ba shi aka ba belin barayin ba.

PREMIUM TIMES ta gano cewa jami’an SSS sun damke lauyan bayan da aka nemi wadanda ake tuhuma din da garkuwa aka rasa, a ranar kokawa kotu.

Haka kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa an damka wa Cif Joji takarda mai dauke da sa hannu, hotuna da adireshin wadanda suka karbi belin ‘yan bindigar, tare kuma da takarda daga Hakimin Kankara, duk ‘yan gidogar suka shirya wa Cif Joji.

Share.

game da Author