SUNAYE: Sabbin Shugabanni kananan hukumomin Zamfara da Matawalle ya nada

0

Gwamnan jihar Zamfara ya nada sabbin shugabannin kananan hukumomin Zamfara 14 ranar Juma’a.

Matawalle ya ce an sauke wadanda suke kai ne bayan an same su day laifin yin almundahada da yin babakere da kudaden kananan hukumomin jihar.

Ahmed Anka – Karamar Hukumar Anka, Makau Karamar Hukumar Bakura, Muhammad Umar, Karamar Hukumar Birnin Magaji, Nasiru Zarumi Masama Karamar Hukumar Bukkuyum.

Abdulazeez Ahmed Karamar Bungudu, Ibrahim Ibrahim Karamar Gummi, Sanusi Karamar Hukumar Gusau, Salisu Dangulbi, Karamar Hukumar Maru.

Shehu Faru Karamar Hukumar Maradun, Lawali Abdullahi, Kauran Namoda, Sani Shinkafi, Shinkafi, Abubakar Musa, Karamar Hukumar Talata-Mafara.

Bayan shugabannin kananan hukumomi, an nada sabon kwamishinan ma’aikatar Kimiyya da fasaha Lawal Abubakar, sannan akwai manyan sakatarori uku,

Lawal Abubakar Maradun, Garba Gusau, Bala Umar.

Share.

game da Author