KORONA:Dalilin rufe asibitin gidan gwamnati ofishin sakataren gwamnati jihar Gombe

0

Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana cewa dalilin rufe ofishin sakataren gwamnatin jihar da asibitin dake fadar ya biyo bayan zargin wani ma’aikacine da aka samu yana dauke da cutar Korona Bairos.

Shuaibu Danlami dake aiki a ofishin sakataren gwamnatin jihar ya kamu da cutar kuma ya rasu a asibitin gidan gwamnati a jihar.

Kakakin gwamnan jihar Ismaila Misilli
ya Sanar da haka ranar Alhamis.

Misilli ya ce ma’aikatan kiwon lafiya sun fara yin bincike domin gano wadanda ake zaton sun yi mu’amula da marigayin a lokacin da yake kwance ba shi da lafiya.

Ya kuma ce za a yi feshi a asibitin da ofishin sakataren gwamnati domin kashe kwayoyin cutar.

Bayan haka shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar ta jihar Idris Mohammed ya ce Shuaibu Danlami na daya daga cikin mutum uku da suka kamu da cutar a jihar ranar Laraba.

Mohammed ya ce gwamnati ta dauki matakan da za su taimaka wajen hana yaduwar cutar a jihar.

“Bincike ya nuna cewa cutar ta fara yaduwa cikin mutane a jihar domin mutum biyu cikin mutum bakwai da cutar ta kashe a jihar ba su da tarihin yin tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin kasar nan.

Gwamnan jihar Inuwa Yahaya ya ce gwamnatin sa zata inganta asibitin yin gwajin cutar dake jihar.

Share.

game da Author