Bana tsammanin Buhari ne ke mulkin Najeriya, ba shi bane – Inji Soyinka

0

Fitaccen marubuci, Wole Soyinka ya bayyana cewa yana da yakinin ba Buhari bane ke mulkin Najeriya a halin yanzu kamar yadda alamu duk suka nuna.

” Ina da tabbacin cewa babu wani yanzu haka dake fadar gwannati a Abuja, wato Aso Rock da yake jagorancin Najeriya.” Haka Soyinka ya fadi a hira da yayi Talbijin di Plus TV Africa ranar Alhamis.

” Za fa ayi hakuri da abin dazan fadi, domin a tsawon shekara daya da rabi da nake yin nazarin yadda abubuwa ke gudana a kasar nan, Ina tabbatar muku cewa ba Buhari bane ke mulkin Najeriya.

Soyinka ya mara wa Buhari baya a 2015, amma kuma kafin 2019, ya yi watsi da wannan soyayya da yake wa Buhari, ya rika sukar gwamnatin yana mai cewa ba ta tabuka komai ba a tsawon shekarunta na mulki sannan bata tabuka abin azo a agni ba ga ‘yan Najeriya.

Sannan Kuma ya yaba wa tsohon gwamnan Kaduna Umar Dangiwa bisa budaddiyar wasikar da ya yi wa shugaba Buhari in ya soki yadda ya ke nuna bangaranci a wajen nade-naden sa.

” Jinjina ga mutane irin su Umar wanda ba su tsoro, za su fito su tsage gaskiya yadda take, ba tare da sun ji tsoro ko kuma fargabar wani abu ba.

” Akwai masu rubuce-rubucen wasika ga shugaban kasa, amma na Umar ya fita dabam da na saura, bai nuna ban garanci ba, sannan kuma ba wai yayi don yana son wani abu ba ne, a bashi ko ayi masa.

” Nuna bangaranci a nade-naden Buhari ya fito fili karara, musamman a fannin ma’aikatar harkokin man fetur ta kasa wanda shine da kansa ke shugabantar wannan ma’aikata.

” Ina ganin ya kamata a hukunta wadanda ke da alhakin aikata irin wadannan abubuwa dake nuna bangaranci a fili kan yadda ake nada manyan jami’an gwamnati a karkashin mulkin Buhari.

Share.

game da Author