Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’in kasar nan, JAMB, ta fidda jerin sunayen jami’o’i 10 da ‘Yan Najeriya suka fi nema a shekarar 2020.
Ga jerin Jami’o’in
1 – Jami’ar Ilori – Jami’ar Ilori ce jami’ar da ta fi yawan dalibai da suka nemi shiga a 2020 domin yin karatu.
Dalibai 103, 582 suka nemi shiga jami’ar.
2 – Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Dalibai 82,984 suka nemi shiga jami’ar.
3 – Jami’ar Legas dake Ikko.
Dalibai 74,800 suka nemi shga jami’ar a 2020.
4 – Jami’ar Bayero dake Kano
Dalibai 70, 376 suka nemi shiga Jami’ar a 2020.
5 – Jami’ar Najeriya dake, Enugu.
Dalibai 68, 971 suka nemi shiga jami’ar a 2020.
6 – Jami’ar Benin, jihar Edo
Dalibai 68,805 suka nemi shiga Jami’ar.
7 – Jami’ar Ibadan, Jihar Oyo.
Dalibai 58,914 suka nemi shiga jami’ar a 2020.
8 – Jami’ar Obafemi Awolowo
Dalibai 58,914 suka nemi shiga jami’ar
a 2020.
9 – Jami’ar Nnamdi Azikwe dake Awka
Dalibai 58,292 suka nemi shiga jami’ar.
10 – Jami’ar Jos, Jihar Filato
Dalibai 57,318 suka nemi shiga jami’ar a 2020.
Discussion about this post