Zamfara ta yi nasarar samar wa Jami’ar Jihar naira bilyan daya daga Hukumar Tetfund

0

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta samu nasarar samar wa Jami’ar Jihar Zamfara naira bilyan 1, daga Asusun Hukumar Bunkasa Jami’o’i ta Kasa (Tetfund).

Jami’ar Jihar Zamfara dai ta na Talata Mafara ce, garin da ke kan titi daga Gusau zuwa Sokoto.

Kakakin Yada Labarai na Gwamna Matawalle, mai suna Zailani Baffa, shi ne ya sanar da haka a cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, a Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara.

Ya yi wannan karin bayani ne dangane da wata tambaya da aka yi masa kan ci gaban da aka samu a jihar bayan hawan Matawalle gwamna a Zamfara.

Ya ce Gwamnatin Matawalle ta ci gadon aikin ginin jami’a daga gwamnatin da ta gabata.

Ya ce saboda haka ba zai yi watsi da aikin ba, shi ya sa zai kammala shi. Kuma tuni har ya kafa wa jami’ar jami’an gudanarwa. Kuma ana ci gaba da daukar matakan kara yi wa jami’ar kakkarfan ginshiki.

“Baya ga ci gaba da aikin jami’a, wanna gwamnati ta Samar wa dalibai 200 guraben karo kwas na ajkin likita, magunguna da sauran fannonin kimiyya, a China, Indiya da Sudan.”

Gwamnatin inji shi ta gina ajujuwa 600 da gyara wasu 300 duk na firamare.

Ya ce kuma har tebura da kujeru duk sun zuba a ajujuwa.

Share.

game da Author