Barno ta horas da likitoci 30, ma’aikatan jinya da ungo zoma 100 a jihar

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Barno Salisu Kwaya-Bura ya bayyana cewa a cikin shekara daya gwamnati ta horas da likitoci 30, ma’aikatan jinya da ungo zoma 100 a jihar.

Kwaya-Bura ya fadi haka wa manema labarai da yake bayanin irin ayyukan ci gaba da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi a jihar cikin shekara a garin Maiduguri ranar Alhamis.

Ya kuma ce gwamnati ta dawo da ma’aikatan kiwon lafiya 200 da suka hada da ma’aikatan jinya da na ungozoma domin inganta aiyukkan aisibitocin gwamnati dake jihar.

Kwaya-Bura ya ce gwamnati ta kara yawan daliban da makarantar koyar da jinya da ungozoma dake jihar daga 50 zuwa 100.

Bayan haka Kwaya-Bura ya ce gwamnati ta kammala gina cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 12 daga cikin 37 da ta yi alkawarin ginawa a kananan hukumomi 17 a jihar.

Ya kuma ce gwamnati ta inganta asibitin mahaukata da babban asibitin Biu.

Game da cutar koda da ya addabi mutane a jihar gwamnati ta kafa kwamiti domin tsara hanyoyin dalike yaduwar cutar sannan gwamnati na kula da wadanda ke fama da wannan ciwo kyauta a jihar.

Gwamnati ta kuma siyo motocin daukar Marisa lafiya guda 18 da yanzu haka suna aiki a asibitocin kasar.

Yaki da cutar Covid-19

Kwaya-Bura ya ce gwamnati ta dauki wasu matakai da suka taimaka wajen rage yaduwar cutar korona a jihar.

“Gwamnati ta killace wadanda suka kamu da cutar amma ba su fara nuna alamun cutar ba a gidajen su tare da aikawa da ma’aikatan kiwon lafiya wanda Za su rika duba su.

“Yin haka ya taimaka wajen kawar da matsalar samun cinkoson mutane a asibitocin killace mutanen da suka kamu da cutar.

Kwaya-Bura ya kuma ce rashin kiyaye dokar hana tafiya da gwamnati ta saka na cikin matsalolin da ya sa cutar Covid-19 ta dada yaduwa a jihar.

“Gwajin cutar da aka yi wa duk wanda ya shigo jihar ya taimaka wajen gano mutanen da suka kamu da cutar.

A yanzu dai mutum 457 ne ke dauke da cutar a jihar.

Share.

game da Author