Mashawarcin Shugaban Kasa a fannin tsaro, Mohammed Monguno, ya bayyana cewa sabbin hare-haren da ‘yan Boko Haram ke kaiwa a Arewa maso Gabas, ya na kara jefa sojojin Najeriya cikin tsaka mai wuya.
Monguno ya yi wannan furuci a Barno, Babban Birnin Jihar Barno, wurin kaddamar da rabon motoci da kayan asibiti ga sojoji, wanda Hukumar Bunkasa Yankin Arewa Maso Gabas ta yi.
“Saboda dalilai masu tarin yawa, sabbin hare-haren da Boko Haram ke kaiwa, musamman bayan ganin cewa shekarun baya an dakile su, abin damuwa ne matuka a wurin sojojin mu.” Inji Monguno.
Duk da dai bai bayyana dalilan da sojojin suka shiga damuwa ba, ya kara da cewa akwai matukar bukatar kowa ya nuna wa sojoji goyon baya, domin su yi nasara.
“Kowane irin taimako ko tallafin agaji daga kowace jihar, duk za mu yi marhabin lale da shi, musamman irin wannan kokari da Hukumar Bunkasa Yankin Arewa ta bayar ga sojojin.”
A wurin taron dai an raba mitoci 70 ga sojoji, guda 30 ga ‘yan sanda, 10 ga SSS, sauran kuma aka raba su ga Asibitocin Gwamnatin Tarayya takwas da ke Shiyyar Arewa Maso Gabas.
A wurin taron har da Ministar Harkokin Agaji da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Faruq da kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, Wanda Sanata Ali Ndume, kuma Shugaban Kwamitin Tsaro ya wakilta.