Ministan Harkokin Kasashen Waje Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa gwamnati ta dawowa da ‘yan Najeriya 167 daga kasar Afrika ta Kudu sannan a yanzu haka su na hanyar dawowa Najeriya.
Onyeama ya fadi haka ne a shafinsa na tweeter ‘@GeoffreyOnyeama’ a yanar gizo ranar Alhamis.
Ya ce jirgin ya taso daga tashar jiragen sama na O.R. Tambo a Johannesburg.
Onyeama ya ce jirgin zai fara sauke fasinjoji a tashar Nnamdi Azikiwe A Abuja sannan ya nausa zuwa tashar jiragen saman Murtala Muhammed dake Legas domin sauke sauran matafiyan.
“Jirgin Za ta ajiye mutum 45 a Abuja sannan sauran mutum 122 a Ikeja jihar Legas.
Idan ba a manta ba a ranar 28 ga watan Mayu Gwamnatin Najeriya ta dakatar da aikin dawo da ‘Yan Najeriya da suka makale a wasu kasashe, sakamakon hana zirga-zirgar jiragen sama, bayan barkewar annobar Coronavirus a duniya.
Gwamnati ta dakatar da shirin ne domin sake tsarin shirin gaba daya, ta yadda za a samu saukin dawo da su a sawwake da kuma maida kowa gidan sa babu wani wahala.