Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) ta bayyana cewa ba ta gamsu da yadda Gwamnatin Tarayya za ta ware zunzurutun kudi har naira bilyan 13.9 duk ta feshe su wajen sayen maganin kwarin yaki da farin-dango ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa a ranar 12 Ga Yuni, Gwamnatin Tarayya ta amince za ta ware zunzurutun kudi har naira bilyan 13 domin sayen maganin feshin farin-dango a jihohi 12 na Arewacin kasar nan.
Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce Gwamnatin Tarayya na sane da illar da farin-dango ke ci gaba da kan yi a Afrika ta Gabas da kuma Gabas ta Tsakiya.
Nanono ya ce za a yi wannan feshin ne domin a hana farin-dango kassara amfanin gonar da ake kokarin nomawa a daminar 2020.
Jihohin da aka ware kudaden domin yaki da farin-dango, sun hada da Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi da Gombe.
Akwai kuma jihohin Taraba, Yobe da kuma Barno, duk su na cikin wannan tsari.
Yadda Farin-dango Suka Darkako Afrika Ta Yamma:
Makonni biyu baya, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Hukumar Abinci ta Majisar Dinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa farin-dango na daf da mamaye ilahirin gonakin Yankin Afrika ta Yamma, nan da cikin watan Yuni mai kamawa.
FAO ta ce yanzu haka milyoyin farin-dango za su gaba da haihuwa da kyankyashe milyoyin ‘ya’ya a kasashen Ethiopia, Kenya, Sudan, Somalia da yankin Afrika ta Yamma.
“Milyoyin farin-dango na ci gaba da kyankyashe ‘ya’ya su na zugar nausawa Sudan. Abin tsoron shi ne idan suka nausa suka mamaye yankin Sahel na Afrika ta Yamma.”
Darakta Janar na FAO, QU Dongyu ya kara da cewa duk wani kokarin daukar matakan da za a iya yi, zai dauki lokaci kafin aiwatarwa.
Ya ce wannan fargabar ta biyo bayan la’akari da irin barnar da farin-dangon suka yi a Sahel har zuwa yankin Yemen.
Ya ce annonar farin ta samu ne sakamakon ruwan sama mai tarin yawa da aka samu shekaru biyu da suka gabata, inda hakan ya bai wa farin sukunin kyankyashe ‘ya’ya masara iyaka.
Kumanin farin-dango bilyan 200,000 suka mamaye kasar Kenya. Kuma an kiyasta cewa a rana daya sukan iya cinye abincin da mutum milyan 84 za su iya cinyewa.
Farin sun yi mummunar barnar dubban daruruwan hektocin gonaki a Afrika ta Gabas.
Hukumar FOA na fargabar cewa yawan farin zai iya nunkawa sau 500 cikin watan Yuni, su yi yawan da za su iya mamaye amfanin gonakin Afrika ta Yamma baki daya, ko ma a ce kasashe 30.
Tuni dai an fara kokarin kaddamar da gidauniyar talladin dala milyan 311.6 domin a yi wa farin-dangon taron-dangi kisa da maganin kwari.
“Mu na bakin kokarin mu, amma aikin akwai wahala kuma zai iya daukar lokaci, tunda dai farin yawon mamaya su ke yi daga nan su nausa can. Za a dauki watanni kafin a kai ga samun nasara.”
Dongyu ya yi maraba da shirin samar da dala milyan 500 da Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin yi domin yaki da farin-dango a Gabas ta Tsakiya da kuma Afrika.
Daga nan ya yi rokon ci gaba da bayar da gudummawa daga masu bayar da gudummawa a duniya.
Fargabar da ake ci gaba da yi shi ne, yadda a yanzu bilyoyin farin-dangon ke ci gaba da kyankyashe bilyoyin ‘ya’ya. Su kuma wadannan ‘ya’yan, nan da cikin watan Yuni za su yi girman da za su rika cinye shuke-shuke komai yawan su a duk gonakin da suka dira.
Hakan inji rahoton zai kara kawo mummnan matsanancin karancin abinci.
“Abin ya zama bugu biyu. Ga annobar Coronavirus ga kuma annobar farin-dango. Su duka za su kawo bala’in karancin abinci.” Cewar Dongyu.
Farin dango a wani rahoton za su cinye abincin mutum milyan 25 a Afrika ta Gabas, a Yemen za su cinye amfanin gona na abincin mutum milyan 17.
Ware Naira Bilyan 13.9 Don Yaki Da Farin-dango Abin Al’ajabi Ne -Manoman Najeriya
Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Najeriya ta bayyana a ranar Alhamis a Abuja cewa ta farka daga barci ta tashi da mamakin jin labarin wai Gwamnatin Tarayya ta ware naira bilyan 13.9 domin yaki da farin-dango.
Shugaban Kungiyar Kabir Ibrahim ya ce abin kunya ne matuka a ce wannan gwamnatin ta na yin irin wannan cinikin-biri-a-sama wanda zai durkusar da harkar noma a kasar nan.
“Ta ya gwamnati za ta ware wadannan irin zunzurutun kudade wai na yaki da farin-dango wadanda ba mu gan su ba. Kirdado da kintace ne fa kawai cewa wai za a yi annobar farin dango a nan gaba.” Ya ce wannan wani abin dai kuma daban,amma ba kokarin bunkasa harkar noma ba.
“Tambaya a nan, ta ya gwamnati ta yi kiyasin kudaden daidai da yawan farin-dangon da aka ce za a yi, alhali ba a ma fara noman ba. Kuma ba a ma ga farin sun shigo ba?”
Daga nan ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa-ido wajen masu tafiyar da harkokin noma da ma’aikatar baki daya, saboda a cewar sa, abin na su ya wuce hankalin masu hankali.