BIDIYO: Yadda yan majalisar Kaduna suka ba hammata iska a zauren majalisa, bayan nada sabon mataimakin Kakaki

0

Mambobin majalisar dokokin jihar Kaduna 24 karkashin jagorancin shugaban majalisar, Yusuf Zailani sun tsige mataimakin shugaban majalisar Mukhtar Hazo.

‘Yan majalisar sun kalubalanci salon mulkin mataimakin shugaban majalisar da hakan yasa suka tsige shi.

Ba a bayyana dalilan tsige shi ba Dalla-Dalla, a zauren majalisar.

Jim kadan bayan ambata tsige mataimakin shugaban majalisar sai aka nada Isaac Zankai dake wakiltar karamar hukumar Kajuru a majalisar sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar.

Bayan haka ‘yan majalisan da basu gamsu da nadin sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar ba sai dambe ya kaure a tsakani. An yayyaga riguna wasu kuma sun sha duka, babu kisa amma dai an yi tirmi.

Kalli yadda yan majalisa suka dambace a zauren majalisa

Share.

game da Author