Mahara sun kashe matafiya biyu, sun yi garkuwa da matafiya a titin Lokoja zuwa Abuja
Wannan hari ya auku ranar Laraba ne wajen karfe 7 na safe tsakanin kauyukan Acheni da Gegu dake jihar Kogi.
Maitaimaka wa gwamnan jihar Kogi kan harkokin yada labarai Mohammed Onogwu ya tabbatar da aukuwar wannan mummunar al’amari a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Lokoja.
Onogwu ya ce wani sannannen attajiri kuma dan kasuwa dake zaune a garin Lokoja, Nicholas Ofodile da wani mutum ne mutane biyun da maharan suka kashe.
A daidai suna arangama da jami’an ‘Yan sanda SARS ne wadannan mutane suka fada inda maharan suka datse.
” Kamar yadda muka samu rahotan abinda ya faru, marigayi Nicholas Ofodile ya kamo hanya daga Lokoja zuwa Abuja a motarsa kiran Lexus SUV, kwatsam sai ya afka wa inda maharan suka datse domin tare mutane.
” Ofodile na afkawa sai suka bude masa wuta nan take ya rasu. Bayan shi sun tare har motoci guda 8. Wasu daga ciki sun ji rauni wasu kuma sun tsira babu rauni sannan sun sace wasu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar William Aya bai ce koma ba game da harin amma ya tabbatar wa’Sahara Reporters’ cewa an kashe mutum biyu a harin da aka yi ranar Laraba.
Bayan haka gwamnan jihar Yahaya Bello ya yi wa ‘yan uwan wadanda suka rasu sannan yayi alkawarin cewa jami’an tsaro za su fantsama domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.