Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa kan iyakokin Najeriya na da marukar wahalar tsarewa.
Ministan ya yi wannan kalami ne yayin da ya ke wa manema labarai karin bayani a Fadar Shugaba Muhamadu Buhari, kadan bayan kammala taron Majalisar Zartaswa na ranar Laraba.
Ya yi bayanin ne dangane da matsalar yawaitar shigowar bakin makiyaya daga makwautan kasashe da kuma yadda harkokin sumogal ke kara bunkasa, duk kuwa da cewa an rufe kan iyakokin kasar nan, saboda fantsamar Cutar Coronavirus.
Zaman yanzu dai makiyaya da kuma harkokin sumogal na tumbatsa, wadanda ake kallo a wata karin barazana ga tsaron kasar nan.
A baya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda harkokin fasa-kwauri ke kara kankama, sakamakon yadda jami’an kwastan ke hada baki da ‘yan fasa-kwauri ana shigo da kayayyaki cikin Najeriya.
“Bari na yi muku bayani, duk da cewa jami’an mu suna kokari wajen kula da kan iyakoki, to akwai wasu kan iyakoki a cikin lunguna, wadanda zai yi wahala saboda yanayin wuraren da su ke a iya kula da su.
“Akwai kan iyakokin da ke kusa da kauyukan wannan kasa da kauyukan makwauciyar kasashe. To irin wadannan yankuna ko an ce za a iya hana jama’a zirga-zirga a.tsakanin su, ba ma zai yiwu ba.”
Haka Aregbesola ya nanata, tare da cewa amma ma’aikatar sa na kokarin ganin ana samun fahimta tsakanin masu rike da sarautun gargajiya da sauran jama’a, wajen taya jami’an tsaro bambance nagari da kuma mugu a cikin al’umma.
Ministan ya kara da cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da kara Inganta dabarun tsaro da kuma kula da kan iyakokin Najeriya ta sama da ta kasa.
Ya ce ana kuma bibiyar yadda makiyaya ke kwararowa a cikin kasar nan daga makautan kasashe, ta yadda a cewar sa har hadin-guiwa sun yi da jami’an ‘yan sanda, SSS, NIA da kuma sojoji.